eMagazine Media Channel News NLC Ta Gudanar da Zanga-Zangar Lumana a Kano dan neman kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.
News

NLC Ta Gudanar da Zanga-Zangar Lumana a Kano dan neman kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

IMG 20251217 084555 421

NLC Ta Gudanar da Zanga-Zangar Lumana a Kano dan neman kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

IMG 20251217 WA0081
Comrade Baffa Ibrahim Garko, Kano State NUT Chairman 

Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta gudanar da zanga-zangar lumana a Kano ranar Laraba 17/12/2025, inda suka yi tattaki daga ɗakin Karatu na Murtala Muhammad zuwa Gidan Gwamnati, suna kira da a mai da hankali sosai kan tabarbarewar tsaro a fadin Najeriya.

NUT REPRESENTATIVES

Shugaban Sashen Ilimi na Hedikwatar NLC ta ƙasa da ke Abuja, Dr. Muttaka Yusha’u, ne ya jagoranci wannan zanga-zanga a madadin Shugaban ƙasa na ƙungiyar, Comrade Joe Ajaero.

Zanga-zangar ta kai ga mika wata wasika da cikakken rahoto ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, inda suka bukace shi da ya isar da korafe-korafen ma’aikata zuwa ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

 

 

A lokacin da yake jawabi ga mahalarta wannan zanga-zanga, Dr. Muttaka ya jaddada gaggawar buƙatar samun hadin kai da tsari mai kyau wajen magance ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta. Ya ce, “Muna nan a Kano bisa shawarar NLC na gudanar da zanga-zangar lumana domin samar da zaman lafiya a ƙasar nan.”

 

Ya kuma yi kira da a dauki matakan gaggawa da domin magance matsalar tsaro a Najeriya.

Ya sake cewa, idan Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ɗauki matakin hadin guiwa, za a iya samun ci gaba mai ma’ana a fadin ƙasa. “Mun zo nan ne don mika wannan gajeren sakon daga ƙungiya domin jawo hankali kan matsalar tsaron da ke shafar al’ummarmu.”

 

Comrade Riruwai ya yaba da jajircewar Gwamnatin Kano wajen kula da jin daɗin ma’aikata . Kuma muna da tabbacin cewa, duk da ƙalubale, gwamnati za ta yi nasara. Domin Kuna yi wa ma’aikata babban aiki, kuma ba mu da wata nadama wajen yin aiki tare da ku,”

Comrade Riruwai ya yaba da matakin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka na ganawa da shugabannin ƙungiyoyin kwadago, inda ya lura da cewa Shugaban Ƙasa ya gayyaci wakilai zuwa Fadar Shugaban Ƙasa tare da bayar da umarnin kafa kwamitin da zai fuskanci hauhawar matsalar tsaro a fadin ƙasa.

 

“Abin farin ciki ne ganin cewa Shugaban Ƙasa ya ɗauki mataki ta hanyar bayar da umarni na kafa kwamiti domin magance matsalar tsaro,” in ji Riruwai. “A matsayarmu na ƙungiyar kwadago, muna magana idan mun gamsu, haka kuma idan ba mu gamsu ba. A yau, mun zo nan ne don bayyana damuwarmu da kuma godiyarmu.”

 

Ya jaddada cewa tsaro shi ne ginshiƙin kowane ƙasa. “Babu wata ƙasa da za ta iya wanzuwa ba tare da tsaro ba. Muna da sa’a a Kano kasancewar muna cikin zaman lafiya mai ɗorewa, kuma muna ganin cewa gwamnati na ƙoƙari sosai wajen kula da wannan zaman lafiya.”

 

Riruwai ya kuma bayyana barazanar da fararen hula da jami’an tsaro ke fuskanta. Kuma akwai buƙatar ƙarin kayan aiki da tallafi ga waɗanda ke kan gaba a fagen fama. “Mutane na rasa rayukansu, har ma da jami’an tsaro ana kashe su. Ta yaya za su yi aikinsu yadda ya kamata idan suna fuskantar irin waɗannan barazanar?”

Baba Comrade, E-Magazine

Daga Gidan Gwamnatin jahar Kano.

17/12/2025

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version