GSS Unguwar Gano Ta Kaddamar da Ƙungiyar Khuddamul Masajidi Domin Inganta Tarbiyya da Hidimar Masallaci
Makarantar Government Secondary School (GSS) Unguwar Gano tare da haɗin guiwa da Ƙungiyar Iyaye da Malamai (PTA) sun kaddamar da wasu ɗalibai a matsayin Khuddamul Masajidi, wato masu hidimar masallacin makarantar. An gudanar da wannan shiri ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Makarantar, Comrade Auwal Yalwa, tare da cikakken goyon bayan shugabannin PTA.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin, Dr. Nasir Mansur Rudwan ya bayyana cewa an zaɓi waɗannan ɗalibai ne domin su riƙa yi wa masallacin makarantar da masu ibada hidima a lokutan sallah. Ya kuma ce an samar da wannan tsari ne domin gina tarbiyya, ɗa’a da kuma ƙarfafa ruhin hidimar addinin Musulunci a zukatan ɗalibai, musamman ta hanyar kula da masallaci da gudanar da ayyukan ibada.
Ya ƙara da cewa, wannan shiri zai taimaka wajen renon ɗalibai masu kyawawan ɗabi’u, nagartaccen hali da kuma ƙarfafa musu alhakin yi wa al’umma da addini hidima.
A nasa jawabin, Shugaban Makarantar, Comrade Auwal Yalwa, ya bayyana cewa ɗaliban da aka naɗa za su kasance masu zuba ruwan alwala ga ɗalibai kafin lokacin sallah, tare da tabbatar da cewa kowane ɗalibi Musulmi ya gudanar da sallah kafin a tashi daga makaranta.
Ya ce wannan shiri wani ɓangare ne na ƙoƙarin makarantar na inganta tarbiyya, ɗa’a, koyar da jagoranci, da kuma ƙarfafa al’adar hidima da ɗaukar nauyi a tsakanin ɗalibai, domin su zama nagartattun ‘yan ƙasa masu amfani ga addini da al’umma.
