AN KASHE GAWURTACCEN ƊANDABA AWAISU A UNGUWAR DORAYI BAYAN YA YI KWACEN WAYA DA ILLATA MAIWAYAR DA ALMAKASHI.
A ranar Asabar 31/1/2026 aka samu wasu matasa da yin kukan Kura wajan kashe wani Dandaba wanda ya shahara da kwacen waya da haurawa gidajen jama’a a unguwar Dorayi me suna Awaisu Musa ɗanshekara 19.

Matashin da aka kashe mai suna Awaisu wanda ya ke zaune a gidan kakanninsa dake Dorayi kusa da gidan Barrister Wada Bashir daura da yankifi. Awaisu ya yi ƙaurin suna wajan addabar al’ummar unguwar ta Dorayi. Shi dai wannan barawo an same shi ne da rana tsaka wajan misalin ƙarfe 4:00 na yamma ya caka wa wata budurwa wuka a kirji tare da kwace mata waya a daidai Konannan gidan mai kusa da masallacin juma’a na Sheikh Ja’afar. Wanda nan take mutane su ka kawo ɗauki wajan ɗaukan yarinyar da aka yi wa kwace a inda aka garzaya da ita zuwa asibiti. A inda wasu fusatattun mutane da ba a san su ba su ka kashe shi tare da ƙone shi nan take.
Hukumar Yansanda ta ce matar da aka caka wa almakashi ba ta mutu ba, wanda a halin yanzu ta ke asibiti domin kulawar likitoci.
Hukumar ta yansanda ta yaba wa jami’inta wanda ya ba da jininsa wajan ceto rayuwar matar da aka caka wa almakashi.
Ga abun da wasu shaidun gani da ido su ka gaya wa wakilin E-Magazine domin ƙarin bayani

