Politics

APC TA KADDAMAR DA ƘANANAN KWAMITOCI DON SHIRYA BABBAN TARONTA NA ƘASA 2026

IMG 20260212 WA0035
IMG 20260212 WA0035

APC Ta Kaddamar da Ƙananan Kwamitoci Don Shirya Babban Taron Ƙasa na 2026

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanar da amincewa da jerin ƙananan kwamitoci (Sub-Committees) da za su jagoranci shirye-shiryen Babban Taron Jam’iyya na Ƙasa (National Convention) na shekarar 2026, a wani mataki na ƙarfafa tsari da tabbatar da gudanar da taro cikin gaskiya da inganci.

A cewar jam’iyyar, an kafa kwamitocin ne domin su kula da muhimman fannoni da suka haɗa da tsare-tsare, gudanarwa, zaɓe, dabarun sufuri (logistics), tsaro da tsara shirye-shirye, domin tabbatar da cewa taron ya gudana cikin kwanciyar hankali da nasara ba tare da wata tangarda ba.

1772052995405

1772052998975

APC ta jaddada cewa kafa waɗannan kwamitoci na daga cikin shirye-shiryen tabbatar da cikakken bin Kundin Tsarin Mulkin jam’iyya da ka’idojin da aka amince da su, tare da tabbatar da adalci da gaskiya a dukkan matakai.

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga mambobin kwamitocin da su gudanar da ayyukansu cikin natsuwa, ƙwazo da rikon amana, domin cika burin da aka sanya a gaba.

1772053002135

1772053005577

A cikin sanarwar da Felix Morka, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na APC, ya fitar, jam’iyyar ta tabbatar wa mambobinta, masu ruwa da tsaki da al’ummar Nijeriya cewa za ta gudanar da babban taro mai inganci da gaskiya, wanda zai ƙara ƙarfafa dimokuraɗiyyar cikin gida tare da bunƙasa manufofinta na ci gaba.

1772053009520

1772053013761

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *