Education

KUNGIYAR NUT TA DALA TA KAI WA MALAMA BARA’ATU TALLAFIN KUƊIN YI MATA DIALYSIS

Kungiyar NUT ta Dala local government dake Kano ta kai wa Malama Bara’atu tallafi kuɗin yi mata wankin Ƙoda a ranar Talata 09/12/2025.

IMG 20251210 WA0004
Malama Bara’atu

Shugaban ƙungiyar NUT reshen karamar hukumar Dala Comrade Yahaya Ramadan tare da mataimakansa sun kai wa Malama Bara’atu tallafin kuɗin da za a sake yi mata wankin Ƙoda da kuma yi mata aiki a Asibitin ƙashi na Dala Orthopedic saboda matsalar ƙafa. Comrade Ramadan ya yi ƙarin haske akan wannan baiwar Allah wadda na ɗaya daga cikin malaman makaranta na ƙaramar hukumar Dala da ke koyarwa a makarantar Khairulwara Islamiyya Primary School.

IMG 20251210 WA0005
Comrade Yahaya Ramadan

NUT Dala Chairman

Comrade Ramadan ya sanar da E-Magazine Media Channel ce wa, ” Ita fa Malama Bara’atu na ɗaya daga cikin malaman makaranta da karamar hukumar Dala ta ke alfahari da su. Wanda hakan ne ya sa ƙungiyar NUT ta Dala ta kawo mata ɗauki na ₦50,000 domin a yi mata aiki da su wajen yi mata magani ba wai dan ta isa ba.

Comrade Ramadan ya ƙara da ce wa, ƙungiyar NUT a shirye ta ke kullum wajan ganin ta taimaka wa malaman makaranta bisa umarnin uwar-ƙungiya ta jahar Kano bisa jagorancin Comrade Baffa Ibrahim Garko .

Baba Comrade, E-Magazine

10/12/2025

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *