eMagazine Media Channel News YJCASYN TA NAƊA COMRADE BAFFA IBRAHIM GARKO A MATSAYIN MAJIDAƊIN-MALAMAI
News

YJCASYN TA NAƊA COMRADE BAFFA IBRAHIM GARKO A MATSAYIN MAJIDAƊIN-MALAMAI

IMG 20260113 WA0013

Ƙungiyar Matasa ‘Yanjarida ta Karrama Shugaban NUT Kano Bisa Gudunmawarsa Ga Ilimi tare da naɗa shi a matsayin majidadin-malamai

Ƙungiyar Youth Journalists Concepts Advocating for Support of Youth of Nigeria (YJCASYN) ta karrama Shugaban Ƙungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT), reshen Jihar Kano, Comrade Baffa Ibrahim Garko tare da naɗa shi a matsayin majidadin malaman makaranta a wani taro da aka gudanar a makarantar Government Girls College (GGC) Kano.

IMG 20251230 WA0042
Comrade Baffa Ibrahim Garko 

Ƙungiyar ta bai wa Comrade Baffa lambar yabo ta musamman tare da naɗa shi da matsayin “Majidadin malamai,” bisa ƙoƙarinsa na ci gaba da tallafa wa harkar ilimi da kuma kare haƙƙin malamai ba dare ba rana.

A nasa jawabin Shugaban ƙungiyar YJCASYN, Comrade Lamilu Hassan, ya bayyana cewa karramawar ta zo ne sakamakon irin ƙwarewa da jajircewar shugabancin Comrade Baffa wajen jagorantar malamai don sauke nauyin koyarwa yadda ya kamata, da kuma taimaka wa ɗalibai wajen koyon sana’o’in dogaro da kai bayan sun kammala karatu.

A madadin Comrade Baffa Ibrahim Garko, Comrade Kabiru Garba Fagge ya tabbatar da cewa,  ƙungiyar NUT tana tare  da dukkan manufofin wannan ƙungiya ta matasan ‘yanjarida. Haka kuma ya bukaci ƙungiyar da ta ƙara ƙaimi wajen tallafa wa ɗalibai su samu sana’o’in dogaro da kai.

Comrade Fagge ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jahar Kano a madadin Comrade Baffa Ibrahim Garko da ta ƙarfafa aiwatar da shirin koyar da sana’o’i a makarantu a fadin jihar, domin taimaka wa ɗalibai su samu hanyar dogaro da kai a rayuwarsu.

Baba Comrade, E-Magazine

13/1/2026

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version