’Yansanda sun kama mutane biyu kan kisan mutum a Dorayi, sun sha alwashin kama duk masu hannu a rikicin daba
Rundunar ’Yansandan Najeriya ta samu nasarar kama mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan wani mutum a unguwar Dorayi Garejin Kamilu da ke Jihar Kano.

Lamarin ya faru ne ranar Talata, 25 ga watan Agusta, 2026, da misalin ƙarfe 8:00 na dare, lokacin da ake zargin wasu ’yan daba sun yi arangama.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya fara ne bayan wani mazaunin yankin ya shiga wani lungu, inda wasu da ake zargin ’yan daba ne, waɗanda ba sa shiri da shi, suka kai masa hari tare da caka masa wuƙa.
Bayan ya samu damar tserewa ya koma wajen ’yan uwansa, sai suka mayar da martani, lamarin da ya sake haifar da wani rikici tsakanin ɓangarorin.
Da yake magana kan lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano (PRO), SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce jami’an ’yan sandan da suka isa wurin domin kawo ɗauki sun tarar da gawar wani mutum da aka kashe bayan an caka masa wuƙa a ƙirji.
Kiyawa ya tabbatar da cewa an kama mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kama sauran waɗanda ake zargin suna da hannu a rikicin.
Ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin Jihar Kano da ma ƙasar baki ɗaya.
Kakakin ’yan sandan ya kuma yaba wa al’ummar Dorayi bisa haɗin kai da goyon bayan da suke bai wa jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya da yaƙi da miyagun laifuka.
Rundunar ’Yan Sandan ta kuma yi gargadin cewa duk wanda aka gano yana da hannu a rikicin za a gano shi kuma a gurfanar da shi a gaban kotu.