Yanmajalisar dokoki na jahar Kano su biyu sun rasu a ranar Laraba 24/12/2025 a kusan lokaci ɗaya.
Yanmajalisun da suka rasu sun rasu ne a dalilin rashin lafiya. Me magana da yawun Gwamnan jahar Kano DG Sunusi Bature Dawakin tofa ya ce , ɗanmajalisa me wakiltar karamar hukumar Ungogo Alh. Aminu Sa’ad Ungogo shi ne ya fara rasuwa a lokacin da ya ke aiki a majalisar dokokin jahar Kano. Wanda daga bisani bayan awa daya da rasuwar Aminu Sa’ad Ungogo sai kuma aka samu labarin rasuwar abokin aikinsa me wakiltar karamar hukumar Kano Municipal Alh. Sarki Aliyu Daneji
Baba Comrade, E-Magazine
24/12/2025
