Wasu ‘Yan Fansho a Kano Sun Roƙi Gwamna Yusuf da Ya Biya Su Kuɗaɗen Gratuity da su ke Bi, mu na fama da talauci.
Wasu tsofaffin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya a Jihar Kano sun yi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya cika alkawarin da ya ɗauka na biyan su kuɗaɗen gratuity da su ke bi.
‘Yanfanshon, a cikin wani roƙo mai cike da tausayi, sun buƙaci gwamnan da ya girmama alkawarinsa, suna mai jaddada nauyin da ke kansa na ɗabi’a da addini wajen biyan su haƙƙoƙinsu bayan shekaru masu yawa da suka yi suna hidima.
Da yake magana a madadin wasu daga cikin waɗanda suka yi ritaya, Kwamared Malam Sani Adamu Kofar Na’isa, tsohon mamba na ƙungiyar shugabannin makarantun firamare ta ƙasa (AOPSHON), ya bayyana matuƙar damuwarsa kan jinkirin da aka yi na tsawon lokaci. A wata hira da tashar E-Magazine Media Channel, ya bayyana cewa , ya yi kusan shekaru takwas da yin ritaya ba tare da ya karɓi kuɗin gratuity ɗinsa ba.
Comrade ya yi roƙo ga gwamnan inda ya ce: “Mai girma Gwamna, muna roƙon ka da ka taimaka mana wajen biyan haƙƙoƙinmu, musamman duba da halin matsin tattalin arziki da muke ciki a yanzu.”
‘Yanfanshon sun jaddada cewa da dama daga cikinsu na fuskantar wahala wajen jure tsadar rayuwa, tare da roƙon gwamnatin jihar da ta ɗauki matakin gaggawa domin magance halin da suke ciki.
— Baba Comrade, E-Magazine, Maris 20, 2026

