WANI MAGIDANCI YA SAKAWA JARIRINSA SUNAN SHUGABAN ƘASA, AHMAD BOLA TINUBU
Allah Ya azurta wani magidanci mai suna Malam Yasayyadi DanBaba, mazaunin Unguwar Sabuwar Mandawari a Jihar Kano, da haihuwar ɗa namiji, inda ya sanya masa suna (AHMAD) Ahmad Bola Tinubu.
Da yake zantawa da mujallar Magazine, Malam DanBaba ya bayyana cewa ya yi hakan ne saboda ƙauna da soyayyar da yake yi wa Shugaban Ƙasa, Ahmad Bola Tinubu, da kuma yadda yake jajircewa wajen gudanar da ayyukan alheri da hidimtawa al’umma ba tare da tsoro ko kasala ba.
Ya ƙara da cewa:
“Na sanya wa ɗana wannan suna ne domin nuna girmamawa da ƙaunar da nake yi wa Shugaban Ƙasa Ahmad Bola Tinubu, bisa irin ƙoƙarin da yake yi wajen ci gaban ƙasa da walwalar al’umma.”
Hakazalika, ya yi amfani da wannan dama wajen gayyatar ‘yan uwa, abokai da sauran al’umma zuwa taron suna da za a gudanar ranar Alhamis mai zuwa, in shaa Allah.
A ƙarshe, ya yi addu’ar Allah Ya ƙara wa Najeriya zaman lafiya, tsaro, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa, tare da yalwar arziki ga al’umma baki ɗaya.
Malam Yasayyadi DanBaba
☎️ 08069170710


