LABARAI

T.PROGRESSIVE GWALE TA GABATAR DA TARON ADDU’A GA MALAMAI MAGABATA, SUN TAYA MALAMAI MURNAR MAULIDIN NABIYI

IMG 20260826 WA0012
IMG 20260826 WA0012

T.PROGRESSIVE GWALE TA GABATAR DA TARON ADDU’A GA MALAMAI MAGABATA, SUN TAYA MALAMAI MURNAR MAULIDIN NABIYI 

T. Progressive Gwale ta yi taron addu’a ga dukkanin malaman makaranta da su ka rasu na ƙaramar hukumar Gwale domin nema musu gafara a wajan Allah SWT.

Jagoran wannan tafiya ta T.Progressive Comrade Umar ya ce, “wannan taron addu’ar ba shi ne na farko ba kuma ba shi ne na ƙarshe ba” . “Wannan taron addu’a da mu ka gabatar a ranar Laraba 26/8/2026 kuma a farkon wannan wata na zagayowar watan Maulidin Annabi Muhammad SAW , Mun yi wa dukkanin malaman makaranta da su ka rasu musamman irin su Malama Aisha Sani da Malama Binta D Auwal waɗanda suna cikin iyayen wannan tafiya ta T Progressive” .

Umar ya kuma taya dukkanin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar manzon tsira Annabi Muhammad SAW, musamman malaman makaranta na ƙaramar hukumar Gwale a madadin Malam Yusuf Sadi . Ya kuma yi kira ga malaman makaranta na Gwale da su zama cikin ɗa’a da sanin yakamata.

Baba Comrade E-Magazine,

27/8/2026

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *