eMagazine Media Channel Uncategorized Shugaba Tinubu Ya Tsige Sufeton ‘Yan Sanda IGP Egbetokun
Uncategorized

Shugaba Tinubu Ya Tsige Sufeton ‘Yan Sanda IGP Egbetokun

IMG 20260224 WA0122

IMG 20260224 WA0122

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sallami Kayode Egbetokun daga mukaminsa na Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya a hukumance.

Hikima Radio

24/2/2026

Manyan jami’an ’yan sanda da majiyoyi daga Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda sun tabbatar da sanarwar.

Wata majiya ta bayyana cewa, “Egbetokun yaje Fadar Shugaban Ƙasa jiya inda aka umarce shi da ya shirya takardun miƙa mulki.

An ruwaito cewa matakin cire Egbetokun ya samu karɓuwa sosai a tsakanin jami’an ’yan sanda. “Jami’an ’yan sanda sun yi murna lokacin da labarin ya bazu a ranar Litinin. Duk da cewa Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta so ya ci gaba da zama, Shugaban ƙasa ya nace kan hukuncinsa,” in ji wata majiya.

Zaman Egbetokun a matsayin Sufeto Janar ya kasance cike da ce-ce-ku-ce, ciki har da tsawaita zamansa bayan kai wa shekarun ritaya da kuma cika shekarun aiki da doka ta tanada, lamarin da ya jawo muhawara kan karya ƙa’idojin aikin ’yan sanda. Zarge-zargen son zuciya da fifita na kusa da shi ma sun biyo bayansa, inda bincike ya nuna saurin karin girma da ake zargin ba su da tushe a cikin sahunsa, musamman kan Bukola Yemisi Kuti, Babbar Jami’arsa ta Musamman, wadda masu sukar sa ke zargin tana da alaka ta musamman da shi.

Sauran ce-ce-ku-ce sun taso ne bayan rahotannin da suka danganta Naira miliyan 100 daga kuɗin tsaron Jihar Anambra ga Victor, ɗan Egbetokun. Masu sukar lamarin sun nuna damuwa kan yiwuwar karkatar da kuɗaɗen gwamnati don amfanin kai, zarge-zargen da suka jawo matakan shari’a.

Saidai rahotanni daga Rundunar na cewa za’a maye gurbinsa ne da wani jami’i dan jihar Legos.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version