eMagazine Media Channel News Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Kasafin Kuɗi na Naira Tiriliyan 58.47 na Shekarar 2026 ga Majalisar Ƙasa
News

Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Kasafin Kuɗi na Naira Tiriliyan 58.47 na Shekarar 2026 ga Majalisar Ƙasa

Tinubu at National Assembly

Tinubu at National Assembly

Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Kasafin Kuɗi na Naira Tiriliyan 58.47 na Shekarar 2026 ga Majalisar Ƙasa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗi na naira tiriliyan 58.47 na shekarar kuɗi ta 2026 a ranar Juma’a 19/12/2025 ga  Majalisar Tarayya, inda ya bayyana muhimman fannoni da za a mai da hankali a kai cikin tattalin arzikin ƙasar.

A cewar wannan  kasafin kuɗin an ware naira tiriliyan 26.08 don manyan ayyuka (capital expenditure), yayin da za a kashe naira tiriliyan 15.25 a kan al’amuran yau da kullum (ba tare da biyan bashi ba). An tsara kasafin a bisa farashin danyen mai na $64.85 akan kowacce gangar-mai.

Shugaban ya bayyana cewa ana sa ran samun jimillar kuɗaɗen shiga na naira tiriliyan 34.33 a shekarar 2026, yayin da ake sa ran kashe naira tiriliyan 58.18, ciki har da naira tiriliyan 15.52 da aka ware don biyan bashin ƙasa. Wannan ya bar gibi (deficit) na naira tiriliyan 23.85, wanda ke wakiltar kashi 4.28 cikin ɗari na GDP.

Tinubu ya bayyana cewa kasafin ya dogara ne a kan fitar da danyen mai ganguna miliyan 1.84 a rana da kuma musayar dala ɗaya da naira 1,400.

A rabon kuɗin da aka ware wa sassa daban-daban, ɓangaren tsaro da kare lafiyar ƙasa ya fi na kowanne ɓangare. Wanda kuɗin ya  tasamma naira tiriliyan 5.41. Sai ababen more rayuwa da aka ware wa naira tiriliyan 3.56. Haka kuma, an ware naira tiriliyan 3.52 ga fannin ilimi, da kuma tiriliyan 2.48 ga fannin lafiya.

Kasafin da aka yi wa take da “Kasafin Ƙarfafawa, Jimillar Haɓaka da Wadata Guda” ya fi zama na alƙawuran raya ƙasa fiye da kirdadon kuɗi kawai.

Yayin da yake jawabi ga ‘yan majalisar, Tinubu ya ce wannan shirin kasafin yana nuna fifikon gwamnatinsa tare da tabbatar da aniyar cigaba da dorewar kuɗi, gaskiya a harkar bashi, da kuma kashe kuɗi mai inganci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version