eMagazine Media Channel Security PCACC TA KWATO MOTOCIN GWAMNATI DAGA TSOFAFFIN KWAMISHINONI DA SUKA GAZA MAYARWA
Security

PCACC TA KWATO MOTOCIN GWAMNATI DAGA TSOFAFFIN KWAMISHINONI DA SUKA GAZA MAYARWA

1772122214803

1772122214803

PCACC Ta Kwato Motocin Gwamnati Daga Tsofaffin Kwamishinoni Da Suka Gaza Mayarwa

Kano, 26 ga Fabrairu, 2026 – Gwamnatin Jihar Kano (KNSG) ta fara kwato motocin mallakin gwamnati da wasu tsofaffin kwamishinoni suka tafi da su bayan murabus dinsu, a wani mataki na kare dukiyar al’umma da tabbatar da bin ka’idojin aiki.

Rahotanni sun nuna cewa Shugaban Hukumar Karɓar Korafe-Korafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Comrade Sa’idu Yahaya, ne ya jagoranci aikin kwato motocin a ranar Alhamis, 26 ga Fabrairu, 2026.

A cewar shugaban hukumar, ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano ya aikewa da tsofaffin jami’an wasiku domin su mayar da motocin gwamnati da ke hannunsu, sai dai wasu daga cikinsu sun gaza bin wannan umarni, lamarin da ya tilasta daukar matakin kwato motocin ta hanyar hukuma.

Jerin Wasu Da Aka Kwato Motocin Hannunsu

Daga cikin tsofaffin kwamishinonin da aka kwato motocin daga hannunsu akwai:

Tsohon Kwamishinan Tsaro, Air Vice Marshal Ibrahim Umar

Tsohon Kwamishinan Matasa, Mustapha Rabiu Kwankwaso

Tsohon Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata

Tsohon Kwamishinan Jin Kai, Dr. Adamu Aliyu Kibiya

Tsohon Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Nasiru Sule Garo

Hukumar ta jaddada kudirinta na ci gaba da daukar matakai masu tsauri domin kare dukiyar gwamnati da tabbatar da gaskiya da rikon amana a tafiyar da harkokin mulki a Jihar Kano.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar ke kokarin karfafa tsarin da zai tabbatar da cewa dukkan kadarorin gwamnati ana amfani da su ne bisa ka’ida, tare da dakile duk wani yunkuri na anfani da su ba bisa doka ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version