NUT TOFA TA BA WA MALAMAN MAKARANTA TALLAFIN RAMADAN, KAYAN ABINCI DOMIN TALLAFA MUSU
Ƙungiyar Malaman makaranta ta Nigeria (NUT) reshen karamar hukumar Tofa ta raba wa wasu malaman makaranta da shugabanni na kungiyar kayayyakin shan ruwa da kayan abinci nau’in Taliya da Sukari domin taimaka musu a matsayinsu na ‘ya’yan kungiyar.
Shugaban ƙungiyar Comrade Shuaibu ya ce an ba wa wadannan malaman tallafin na watan Ramadan domin su samu sauki wajen hidimar azumi . Shuaibu ya kuma kara da cewa, ba wa malamai irin wannan kayayyakin abinci yana kara musu karfin guiwa a wajan aikinsu na koyarwa.
A karshe shugaban ya yi wa dukkannin malaman makaranta fatan alkhairi tare da fatan Allah ya karɓi ibadummu na watan Ramadan.
Wasu daga cikin malaman da aka ba wa wannan tallafi na watan Ramadan sun nuna godiya da jin daɗinsu akan wannan kokari da akai musu na basu kayan abinci.

