NUT Kura Ta Bai Wa Malamai Tallafin Ramadan
Ƙungiyar Malaman Makaranta ta Nigeria, Nigeria Union of Teachers (NUT) reshen karamar hukumar Kura, ta raba tallafin kuɗi ga mambobinta domin taimaka musu wajen shirye-shiryen shiga azumin watan Ramadan.
An gudanar da rabon tallafin ne a yayin taron ƙungiyar da aka yi a ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban NUT reshen karamar hukumar Kura ya nuna godiya ga mambobin ƙungiyar bisa haɗin kai da goyon bayan da suke bai wa shugabanci. Ya jaddada cewa NUT za ta ci gaba da ɗaukar matakan tallafa wa mambobinta domin inganta jin daɗinsu. Shugaban ya kuma miƙa saƙon godiya ta musamman ga National Vice President Comrade Muhammad Hambali Abubakar bisa goyon baya da taimakawa kungiyar ta Kura da ya ke yi a matsayinsa na uba tare da taya shi murnar samun girman kujerar shugabancin ƙungiyar malaman makaranta daga mataki na 2nd Vice President zuwa 1st Vice President.
A nasa jawabin, ma’aji na NUT na ƙaramar hukumar ta Kura, Malam Shehu Haruna, ya shawarci malamai da su yi amfani da kuɗaɗen da aka raba musu wajen shirye-shiryen kama azumi da kuma bukatun iyalansu.
Haka zalika, Comrade Usman Abdul Malik Matawallen Kura, NUT Auditor 1, ya bayyana farin cikinsa tare da miƙa godiya ga shugabancin ƙungiyar bisa wannan tagomashi da ake yi wa mambobi duk shekara, yana mai cewa wannan tallafi na ƙara ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakanin malamai.
Rahoton ya nuna cewa wannan shiri na daga cikin matakan da NUT reshen Kura ke ɗauka na ƙarfafa walwala da jin daɗin mambobinta, musamman a lokutan bukukuwa da ibadu.
Iliyasu Dauda, Kura

