NUT Kumbotso Ta Ɗauki Nauyin Auren Malamai, Ta Biya Sadaki Don Tallafa wa Jin Daɗin Mambobi
Ƙungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT), reshen Ƙaramar Hukumar Kumbotso, ta taimaka wajen ɗaura auren wasu malamai biyu tare da biyan cikakken kuɗin sadaki a matsayin wani ɓangare na shirinta na kula da jin daɗin mambobinta.
Da yake jawabi kan wannan ci gaba, Shugaban NUT na Kumbotso, Kwamared Sani, ya bayyana cewa ƙungiyar ta ɗauki wannan mataki ne ta hanyar biyan sadakin Malam Sule, wanda ya auri wata malamar makaranta, domin ƙarfafa zaman aure mai ɗorewa a tsakanin malamai.
Ya ƙara da cewa, wannan shiri na da nufin ƙara ƙwarin guiwa da kuma inganta haɗin kai a cikin sana’ar koyarwa, musamman wajen tallafa wa malamai mata da suka rasa mazajensu, waɗanda ke kula da yara ƙanana da marayu.
Kwamared Sani ya kuma bayyana farin cikin ƙungiyar bisa ganin wannan aure da aka yi a tsakanin malamai, yana mai cewa hakan wata kyakkyawar alama ce ta haɗin kai a fannin ilimi a Kumbotso.
Ya yi addu’ar Allah Ya ba ma’auratan zaman lafiya, jituwa da wadata a rayuwar aurensu.
Baba Comrade E-Magazine, Kumbotso – 25 ga Maris, 2025
