Education

ZA MU YI WA MALAMAI 16,634 PROMOTION KAMAR YADDA NUT TA NEMA

images (29)
images (29)

ZA MU YI WA MALAMAI 16,634 PROMOTION KAMAR YADDA NUT TA NEMA

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Amince da Karin Girma ga Malaman Makaranta 16,634.

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da yi wa Malaman Makaranta da sauran ma’aikatan sassan ilimi na Kananan Hukumomi 44 su 16,634 karin girma (Promotion) Kamar yadda Kungiyar ta malaman makaranta ta Nigeria (NUT) ta nema .

Bayanin hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da Daraktan Sashen Lura da Harkokin Sadarwa na Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano (SUBEB), Balarabe Danlami, ya fitar.

Daraktan ya bayyana cewa Shugaban Hukumar SUBEB, Malam Yusuf Kabir, ne ya sanar da wannan albishir yayin da yake jawabi kan batun karin girman, inda ya tabbatar da amincewar Gwamna Abba Kabir Yusuf na biyan dukkan kudaden da suka shafi karin girman.

A cewarsa, Malaman Makaranta da sauran ma’aikatan sassan ilimi 16,634 ne suka amfana da wannan karin girma, wadanda lokacin karin girman nasu ya kama daga watan Yulin 2024 zuwa watan Yulin 2025.

Shugaban Hukumar ya bayyana godiyarsa ga Gwamnan Jihar Kano bisa wannan gagarumin tagomashi, yana mai cewa hakan na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na bunkasa walwalar ma’aikata da kuma inganta harkar ilimi.

Daga bisani, ya yi kira ga Malaman Makaranta da sauran ma’aikatan da suka amfana da wannan karin girma da su kara jajircewa wajen gudanar da ayyukansu, domin taimakawa Gwamnati wajen cimma kudurinta na inganta ilimi a fadin Jihar Kano.

Shugaban ƙungiyar malaman makaranta ta Nigeria NUT reshen Jahar Kano Comrade Baffa Ibrahim Garko ya nuna jin daɗinsa da godiya ga Allah SWT bisa amincewa da wannan bukata tasu da maigirma Gwamnan jahar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya aminta . Garko ya ƙara kira ga gwamnatin jahar Kano da ta yi ƙoƙari wajen ganin an daidaita albashin malaman primary kamar yadda ake biyan sauran malamai na sakandire domin a gudu tare a tsira tare.

Baba Comrade, E-magazine

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *