NUT Kano Ta Dauki Nauyin sama wa malamai 1950 takardar karin girma, an ba wa malamai abinci da abin sha
KANO: Ƙungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT), Reshen Jihar Kano, ta ɗauki nauyin samar da muhimman kayayyaki da abinci ga malaman da ke halartar taron tantance cancantar ƙarin girma na aiki (Promotion Interview) na watan Yuli 2026, wadda Hukumar Kula da Makarantun Sakandaren Gwamnati ta Kano (KSSSSMB) da Hukumar Kula da Ayyukan Malaman Makarantu (STSB) suka shirya.
Ƙungiyar ta kuma samar da dukkan takardu, kayan rubutu, kayan bugawa da sauran abubuwan da ake buƙata domin samar da Professional Notification Letters ga malaman makarantu da ke ƙarƙashin KSSSSMB da STSB.
A cewar NUT Kano, wannan tallafi na daga cikin ƙoƙarin ƙungiyar na ci gaba da tallafa wa ci gaban sana’a da walwalar malamai, musamman a lokacin gudanar da Interview na ƙarin girma da ake gudanarwa a duk bayan watanni shida.
Mambobin Kwamitin Promotion na NUT ne suka miƙa kayayyakin ga KSSSSMB da STSB. Mataimakin Shugaban ƙungiyar NUT na Kano, Comrade Aminu Adamu, ne ya jagoranci tawagar, inda ya wakilci Shugaban NUT Kano, Comrade Baffa Ibrahim Garko.
Sauran mambobin kwamitin da suka kasance cikin tawagar sun haɗa da Comrade Ubale Bala, Mataimakin Shugaba na huɗu; Comrade Shehu Badamasi Gora, National Rep; Comrade Umar Tijjani Isah, Manajan Edita; Comrade Mustapha Sule Gaya, Babban Co-opted Member; da Comrade Auwalu Shuaibu Jae, Co-opted Member.
Tawagar ta miƙa wa shugabannin KSSSSMB da STSB kayayyakin da ake buƙata domin buga Notification Letters na malaman makarantun sakandare, kamar yadda aka saba gudanar da irin wannan aiki a duk bayan watanni shida.
Bayan karɓar kayayyakin, Daraktan Promotion & Discipline na KSSSSMB ya bayyana godiyarsa ga NUT Kano bisa irin goyon bayan da ta ke bai wa hukumar da kuma gudunmawar da take bayarwa wajen samun nasarar gudanar da Promotional Interview.
Daraktan ya bayyana cewa a wannan zagayen na July 2026, KSSSSMB na gudanar da Promotional Interview ga ma’aikata kimanin 5,000.
Haka kuma, NUT Kano State Wing ta samar da kayan ciye-ciye da abubuwan sha ga malaman makaranta da sauran mahalarta da ke halartar hirar Promotion.
Babban Sakatare (Executive Secretary) na hukumar ya yaba wa jami’an da ke gudanar da Interview da kuma wakilan manyan ƙungiyoyin ilimi, ciki har da Nigeria Union of Teachers (NUT), bisa haɗin kai, jajircewa da goyon bayan da suka bayar domin ganin an gudanar da aikin cikin nasara.
Ya kuma yaba da irin gudunmawar da kowa ya bayar wajen tabbatar da cewa an gudanar da Promotional Interview cikin adalci, tsari da sahihanci.
NUT Kano State Wing ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da tallafa wa ci gaban sana’a, ƙarin girma a aiki da walwalar malamai a faɗin Jahar Kano.
Baba Comrade E-Magazine
NUT Kano State Wing
10 ga Agusta, 2026

