KWAMISHINA WAIYA BA ABUN WATSARWA BA NE, MA’AIKACI NE ME KISHIN KANO
A shirye-shiryen bikin karbar Gwamnan jahar Kano da magoya bayansa da jam’iyyar APC ta ƙasa ke shirin gudanarwa a ranar Litinin 16/2/2026 a jahar Kano. An samu wasu rahotanni daga wasu rubuce-rubuce na mikalu da jaridu da su ke nuna cewa, ‘ Akwai Lauje cikin nadi’. Domin tun daga kafa kwamitocin karɓar gwamna an fara nuna san zuciya
A Dalilin wannan hange na masana da dama a harkar siyasa sun fassara wadannan kalamai da cewa, yunkuri ne na kawar da wasu jigajigan gwamnati daga kujerunsu da su ke da mahimmanci ga Gwamnatin jahar Kano da shi kansa Maigirma Gwamnan jahar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf. Idan muka yi duba ga kwamitin Labarai na karbar Gwamnan jahar Kano, za mu ga cewa, wannan yunkuri na canza mutanen Gwamna Abba ya fara aiki. Domin an jingine Kwamishinan Labarai mai ci da maye gurbinsa a jagorancin kwamitin na yada labarai.
Masana da dama sun yi kira ga maigirma Gwamnan jahar Kano da ya sa ido sosai akan duk wani yunkuri na canza masa CABINET nasa ba tare da ra’ayinsa ba.

