Kungiyar malaman makaranta reshen karamar hukumar Kibiya ta kai ziyarar dubiya ga wasu malaman makaranta a ranar Asabar 6/12/2025.
Shugaban kungiyar NUT na karamar hukumar Kibiya Comrade Nasiru Muhd Kibiya tare da mataimakansa ne su ka shirya wannan ziyarar dubiya da jaje ga wasu daga cikin malaman makaranta waɗanda su ka haɗa da malam Musa Mammada wanda aka yi masa aiki a Asibiti akan larurar da ta ke damunsa. Comrade Kibiya ya ce , mun kai wannan Ziyarar ne ga marasa lafiya domin jajanta musu da kuma basu tallafin kuɗaɗen shan magani da kuma yi musu addu’a .
Comrade Kibiya ya ƙara da ce wa, kowanne majinyaci da mu ka je duba shi mun bashi tallafin Naira dubu Ashirin(₦20,000) nan take.
Comrade Dauda Malam ɗauke da rahoto.
