Kungiyar NUT Ta jahar Jigawa ta gudanar da zaɓen Sabbin Shugabanninta na Jaha – Baba Comrade, E-Magazine
Ƙungiyar Malaman Makaranta ta Ƙasa (NUT), reshen Jihar Jigawa, ta gudanar da zaɓen sababbin shugabanni da za su jagoranci harkokin ƙungiyar na tsawon shekara hudu masu zuwa.
An gudanar da zaɓen ne yayin taron wakilai karo na takwas (8th Triennial Delegates Conference) na NUT reshen Jihar Jigawa, wanda aka yi a babban birnin jihar, Dutse.
A yayin bude taron, Shugaban Ƙungiyar NUT, Comrade Titus Audi Amba, ya bayyana cewa ƙungiyar ta samo asali ne daga tsarin dimokuraɗiyya da falsafar ƙwadago.
Ya ce a bisa wannan tsari ne ake gudanar da zaɓe a matakin ƙasa, jihohi da ƙananan hukumomi domin kawo sabbin shugabanni bayan kammala wa’adin shugabannin da ke kan mulki. Saboda haka, lokaci ya yi da za a gudanar da sabon zaɓe a jihar Jigawa a watan Disamba.
Comrade Amba ya jaddada ƙudurin ƙungiyar na ci gaba da fafutukar ganin an inganta jin daɗin malamai da yanayin koyarwa da koyo a Najeriya.
A nasa jawabin, Shugaban NUT na jihar mai barin gado, Comrade Abdulkadir Yunusa, ya ce sun yi aiki kafada da kafada da gwamnatin jihar don gyara fannin ilimi.
Ya ce a lokacin mulkinsa, sun kasance abokan hulɗa da gwamnati, lamarin da ya haifar da aiwatar da albashi mafi ƙaranci na N70,000, biyan basussuka, fansho da sauran haƙƙoƙi akan lokaci.
“An aiwatar da manufofi da dama tare da haɗin guiwar gwamnati da sauran abokan hulɗa, wanda hakan ya inganta sakamakon koyo a fadin jihar.
“Ina roƙon sababbin shugabanni su ɗauki darasi daga nasarorin da muka samu, su kuma inganta inda muka fuskanci ƙalubale,” in ji shi.
A jawabinsa na karɓar shugabanci, sabon shugaban NUT da aka zaɓa, Comrade Dauda Alhaji Shuaibu, ya yi alƙawarin yin aiki tare da dukkan membobin ƙungiyar da masu ruwa da tsaki domin sake fasalta ƙungiyar zuwa wacce za ta mayar da hankali kan walwalar malamai da kare mutunci da kwarewar aikin koyarwa a jihar.
Sauran sabbin shugabannin da aka zaɓa sun haɗa da: Auwal Sabo – Mataimakin Shugaba, Auwal Magaji – Na farko a matsayin Mataimaki, Masudu Ismail – Na biyu, Muawiya – Na uku, Isah Muhammad – Na huɗu, Aminu Hafiz – Mai binciken cikin gida na farko, Lawan Ilu – Mai bincike na biyu, da Zakar Shehu – Sakataren Yaɗa Labarai.
Sauran sun haɗa da Auwal Uba – Sakataren Huldar Jama’a, Maryam Lawan Abubakar – Mataimakiyar Sakataren Huldar Jama’a, Arms Muhammad – Wakilin Ƙasa na Jihar, da Nura Dahiru – Edita.
Baba Comrade, E-Magazine
Daga jahar Jigawan Nigeria
19/12/2025
