Education

KUNGIYAR BESDA COHORT IV SUN KARRAMA SHUGABAN ƘUNGIYAR MALAMAN MAKARANTA NA JAHAR KANO COMRADE BAFFA IBRAHIM GARKO

aiposter 2025 12 16 023600
aiposter 2025 12 16 023600

aiposter 2025 12 16 023600

Ƙungiyar malaman BESDA na karo hudu waɗanda aka maida su ma’aikata na dundundun (Permanent staff) sun karrama shugaban ƙungiyar malaman makaranta na jahar Kano Comrade Baffa Ibrahim Garko.

A ranar Talata 16/12/2025 tsohuwar kungiyar yanbesda COHORT IV su ka kawo wa shugaban kungiyar malaman makaranta na jahar Kano comrade Baffa Ibrahim Garko tare da bashi certificate na karramawa.

aiposter 2025 12 16 023925

Sakataren Kungiyar mal. Munzali Iliyasu ya ce , sun kawo wannan ziyara ne saboda nuna goyon bayansu ga kungiyar NUT tare da nuna jin daɗinsu akan yadda shugaban ƙungiyar NUT na jahar Kano comrade Baffa Ibrahim Garko yai gauro yai mari wajan tabbatar da sama musu OFFER ta ɗaukan aiki ta dundundun. Mal. Iliyasu ya ƙara da cewa , ” hakika za mu rama kyauta da tukuici , wajan ganin Gwamnan jahar Kano ya maimaita kujerarsa.”

IMG 20251216 142507 840

IMG 20251216 142346 805

Mal. Iliyasu ya ce, ” ba mu da uban da ya wuce Comrade Baffa Ibrahim Garko a wannan harkar ta koyarwa” ” kuma ba mu da kungiyar da ta wuce NUT.

Baba Comrade, E-Magazine

@nutkanopress, 16/12/2025

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *