KOMC Ta Taya Gwamna Abba da Waiya murnar samun lambar Girma da aka ba wa Gwamna Abba akan taimakon Fannin Aikin Jarida da ya ke yi
Ƙungiyar Kano Online Media Chapel (KOMC) ta Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) ta taya Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Abba Kabir Yusuf, da Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, murnar karrama Gwamnan bisa goyon bayan da yake bai wa aikin jarida.
An bayyana wannan yabo ne a cikin wata sanarwar ƙarshe da aka fitar bayan taron majalisar (Congress) na Chapel ɗin da aka gudanar ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2026, a Cibiyar ’Yan Jarida ta NUJ, Jihar Kano.
Taron ya kuma yanke shawarar ƙara ƙarfafa aikin jarida na ƙwarewa, inganta walwalar mambobi, tabbatar da ɗorewar harkokin kuɗi, da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin ’yan jaridar kafafen intanet a jihar.
Chapel ɗin ta buƙaci mambobinta da su riƙa bin ƙa’idojin aikin jarida na NUJ, musamman wajen bayar da rahotanni kan harkokin siyasa da zaɓe, tare da tabbatar da sahihanci, adalci, daidaito da kuma ɗaukar nauyin da ya rataya a wuyan ɗan jarida wajen rahotanninsu.
Haka kuma, Chapel ɗin ta amince da kafa Kwamitin Tattara Kuɗaɗen Shiga mai mambobi bakwai, da tsarin bayar da gudummawar kuɗi na wata-wata daga mambobi, da kuma kafa tsarin “Rate Card” domin ayyukan da suka shafi tallace-tallace.
Taron ya kuma amince da gudanar da bikin cika shekaru biyu da kafuwar Chapel ɗin.
Bugu da ƙari, Congress ɗin ya yanke shawarar tattaunawa da Majalisar NUJ ta Jihar Kano kan bayar da katunan shaidar zama memba ga mambobin Chapel ɗin, tare da yin kira ga mambobi da su ƙara shiga cikin ayyukan Chapel ɗin.
Shugaban Chapel ɗin, Comrade Abubakar Abdulkadir Dangambo, da Mataimakin Sakatare, Comrade Sunusi A. Kofar Na’isa, ne suka sanya hannu kan sanarwar.

