ASUSS KANO TA BAI WA MALAMAN DA AKA GIRMAMA KYAUTAR KUƊI, KWAMISHINAN ILIMI DA SAKATAREN ZARTASWA NA KSSSSMB SUN YABA WA KUNGIYAR.
Ƙungiyar Malaman Makarantun Sakandare ta Jiha (Academic Staff Union of Secondary Schools – ASUSS), reshen Jihar Kano, ta bai wa malaman da suka cancanci kyautar kuɗi Naira 5,000 kowannensu, waɗanda Hukumar Kula da Makarantun Sakande ta Jihar Kano (KSSSSMB) ta karrama saboda ƙwazo da gudummawar da suke bayarwa wajen bunƙasa ilimi.
Wannan mataki ya samu yabo daga Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Gwani Dr. Ali Haruna Makoda, da Babban Sakataren Zartarwa na Hukumar KSSSSMB, Hon. Rabi’u Sale Gwarzo.
An gabatar da kyaututtukan ne a wani biki da hukumar KSSSSMB ta shirya domin karrama malaman da suka nuna jajircewa, sadaukarwa da kuma gagarumar gudummawa wajen ci gaban harkokin ilimi a Jihar Kano.
Da yake jawabi a wajen taron, Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Gwani Dr. Ali Haruna Makoda, ya yaba wa ASUSS bisa tallafa wa shirin karrama malaman da suka cancanta.
Kwamishinan ya bayyana cewa irin wannan kyakkyawan mataki zai ƙara ƙarfafa wa malamai guiwa wajen sauke nauyin da ke kansu, tare da himmatuwa domin inganta ayyukansu da samar da ingantaccen ilimi.
Ya sake jaddada aniyar Gwamnatin Jihar Kano na inganta ƙa’idojin koyarwa da ƙarfafa ɓangaren ilimi ta hanyar aiwatar da shirye-shiryen da ke haɓaka ƙwarewar malamai da kuma amincewa da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen ci gaban al’umma.
A nasa jawabin, Babban Sakataren Zartarwa na KSSSSMB, Hon. Rabi’u Sale Gwarzo, ya nuna godiyarsa ga ASUSS bisa wannan kyakkyawar gudummawa, yana mai bayyana cewa irin wannan tallafi zai taimaka wajen ƙarfafa wa malamai guiwa da kuma bunƙasa ƙwazo a makarantun sakandare na gwamnati.
Haka kuma, Shugaban ASUSS na Jihar Kano, Comrade Dr. Abdu Usman Yalo, ya sake tabbatar da aniyar ƙungiyar na inganta jajircewar malamai da kuma ƙarfafa al’adar bayar da lada ga waɗanda suka yi fice a aikinsu.
Ya bayyana cewa karrama malamai bisa ƙwazon da suka nuna zai zaburar da su wajen ƙara bayar da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban ilimi a Jihar Kano.
Shugaban ya kuma bayyana farin cikin ƙungiyar game da manufofin Gwamnatin Jihar Kano a fannin ilimi, tare da tabbatar da cewa ASUSS za ta ci gaba da tallafa wa ƙoƙarin gwamnati na inganta koyarwa da samar da ingantaccen ilimi a faɗin jihar.
Da suke magana a madadin waɗanda suka amfana da kyaututtukan, Hafsat Muhammad Jakada, Shugabar GGSS Kofar Kudu, da Sunusi Khalid Bello na GGASS Tudun Fulani, sun nuna godiyarsu bisa karramawar da kuma kyautar kuɗin da aka ba su.
Sun kuma yi alƙawarin ci gaba da jajircewa wajen sauke nauyin da ke kansu, tare da bayar da gudummawarsu wajen bunƙasa harkokin ilimi a Jihar Kano.
Taron ya samu halartar daraktocin hukumar KSSSSMB, wakilan ASUSS, Ƙungiyar Shugabannin Makarantun Sakandare ta Ƙasa (ANCOPSS), Ƙungiyar Malaman Najeriya (NUT), da sauran masu ruwa da tsaki a fannin ilimi.
Usman Datti Abdullahi
Darakta, Wayar da Kan Jama’a
KSSSSMB
29/10/2026


