Gwamnatin jahar Kano ta ba wa yanjarida masu amfani da yanar gizo ( Online)horo na musamman akan sanin ƙa’idoji da dokokin aikin jarida na kwanaki biyu a Manpower Development Institute dage Dutsen jahar Jigawa.

Hukumar yaɗa labarai ta jahar Kano bisa jagorancin Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya ta shirya wa mambobin ƙungiyar yanjarida masu amfani da yanar gizo horo na musamman domin bunƙasa aikin jarida ta yadda kowanne ɗanjarida zai samu ƙarin kwarewa da kuma sanin ƙa’idoji da dokokin aikin jarida ta kafar sadarwa na zamani (social media). Waiya ya ja kunnen yanjaridu masu amfani da yanar Gizo (Internet) da su yi ƙoƙari su yi aiki da abubuwan da aka koya domin kare mutuncin aikin jarida ta yadda za a kauce wa yaɗa labaran ƙarya.
Waiya ya ce mun gayyato kwararrun malamai masana daga jami’ar Bayero guda takwas , domin su ba ku wannan bita maimahimci a matsayinku na masu yaɗa labarai. Malaman da su ka bada wannan horo sun haɗa da:
1- Dr. Saminu Umar (phD), ya gabatar da paper mai taken ‘Online journalists for sustainable development in Kano State.’
2- Dr. Hassan Alhaji Ya’u (phD), ya gabatar da paper mai taken ‘Global Best Practices in Digital Journalism’
3- Professor Nura Ibrahim, ya gabatar da paper mai taken ‘Techniques of Use of Language in Multimedia journalism.”
4- Malam A. Yushe’u Shuaibu, ya gabatar da paper mai taken ‘Monetization Strategies and Grant Opportunities for Sustainable Online Journalism.’
5- Comrade Abbas Ibrahim, ya gabatar da paper mai taken ‘Specialized Security and Crime Reporting.’
6- Mr. Musikilu Agbaje Mowed, ya gabatar da paper mai taken ‘Understanding Digital and Investigative Journalism.’
7- Malam Auwal Mu’azu , ya gabatar da paper mai taken ‘Ethical and Legal Considerations in New Media Journalism.’
8- Dr. Aminu Shehu Ibrahim, ya gabatar da paper mai taken ‘ Health Issues and Personal Safety for Online Journalists.’
Shugaban ƙungiyar ta Kano Online Media Chapel Comrade Abdulkadir Dangambo ya yi jawabin godiya da maraba ga dukkanin malaman da su ka bada wannan gudummawa tare da isar da saƙon godiya ta musamman ga maigirma Gwamnan jahar Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa ɗaukan nauyin ba wa yanjarida horo na musamman na kwanaki biyu.
Baba Comrade, E-magazine.
15/1/2026