Ƙungiyar NUT ta jahar Kano ta yi kira ga malaman makaranta da su taya ta addu’a wajan samun nasarar gyaran albashin malaman makaranta.
Ƙungiyar Malaman makaranta ta NUT reshen Jahar Kano ta yi kira ga malaman makaranta musamman na Primary schools da su maida hankali wajan yi musu addu’ar neman nasara a maimakon kushe ƙoƙarin ƙungiyar da ɓata mata suna a shafukan sada zumunta.
Shugaban ƙungiyar Comrade Baffa Ibrahim Garko ya ce, ƙungiyar NUT kullum cikin fafutika ta ke yi wajan ganin an samu daidaiton albashin malaman makaranta. Garko ya ƙara da cewa, ƙofofin NUT a buɗe su ke wajan karɓar shawarwari daga malaman makaranta domin ciyar da ilimi gaba da kuma taimaka wa malaman makaranta a duk faɗin jahar Kano.
Baba Comrade,E-magazine.
15/1/2026

