eMagazine Media Channel News Keta Ka’idar Tsarin Gwamnati: A Girmama Kujera, Ba Mutum Ba
News

Keta Ka’idar Tsarin Gwamnati: A Girmama Kujera, Ba Mutum Ba

IMG 20260211 WA0001

IMG 20260211 WA0001

Keta Ka’idar Tsarin Gwamnati: A Girmama Kujera, Ba Mutum Ba

Daga Mohammed B. Abubakar

Wannan tsari da aka fito da shi na kwamitin yaɗa labarai don karɓar Maigirma Gwamna zuwa jam’iyyar APC, ba kuskure ba ne kawai na shawara, keta alfarmar tsarin mulki ne da ka’idar aiki na kowace gwamnati mai inganci.

A kowace irin gwamnati mai tsari, Kwamishinan Yaɗa Labarai mai ci shi ne muryar gwamnati kuma babban jami’i mai kula da dukkan kafafan yaɗa labarai na jiha. Matakin ɗaukar tsohon jami’i (Ex-Commissioner) a ba shi jagorancin kwamitin, yayin da aka maida Kwamishina mai ci a matsayin memba, wani babban koma-baya ne ga tafiyar mu.

Wannan mataki yana nuna wa duniya abubuwa guda uku:

– Rashin Girmama Zaɓin Gwamna: Rashin bai wa Kwamishina mai ci jagoranci na nufin ba a girmama naɗin da Maigirma Gwamna ya yi masa ba.

– Samar da Gwamnatin Inuwa: Wannan yana nuna akwai wasu mutane da suke ganin sun fi ƙarfin gwamnati mai ci a yanzu.

– Rarraba Kan Jam’iyya: Maimakon wannan karɓar ta zama sanadiyyar haɗin kai, wannan tsari na son zuciya zai haifar da rashin jituwa da zagon ƙasa tsakanin jami’an gwamnati da na jam’iyya.

Ba za mu taba amincewa da tsarin da zai raina ofishin da yake kan aiki ba. Idan har muna son karɓar Maigirma Gwamna ta zama abin alfahari da kishin jam’iyyar APC, dole ne mu mutunta tsarin shugabanci na yanzu.

Muna kira ga jagororin jam’iyya da su gaggauta sake duba wannan tsari domin gujewa kunyata gwamnati a idon duniya. Haɗin kai ba ya samuwa ta hanyar mayar da na yanzu baya, ana tura na jiya gaba.

Mohamed B abubakar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version