BAZA MU LAMUNTA WAIYA SANIYAR WARE BA!
Abin kunya ne a ce za a kafa kwamitin bikin karɓar Mai Girma Gwamna, sai a mayar da Waiya, wanda ya kasance makogwaron wannan gwamnati, a matsayin memba kawai! Wannan ba adalci bane, kuma ba girmamawa ba ce ga jajircewar da ya nuna wajen cigaban gwamnati da jam’iyya.
Idan har muna son zaman lafiya da haɗin kai a APC Kano, dole ne a gyara wannan tsarin nan da nan. Mutum mai gudunmawa irin Waiya ya cancanci jagoranci, ba a ware shi ba.
Muna kira ga shugabancin jam’iyya:
Gyara wannan kuskure, kare martaba da jajircewar Waiya, domin adalci da zaman lafiya a cikin jam’iyya.
Adalci shine ginshiƙin haɗin kai. Ba adalci, ba zaman lafiya!

