eMagazine Media Channel News Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Jihar Kano Ta Dauki Matakin Ladabtarwa Kan Alkalin da Ya Yi Sake a Ayyukansa
News

Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Jihar Kano Ta Dauki Matakin Ladabtarwa Kan Alkalin da Ya Yi Sake a Ayyukansa

Justice dije

Justice dije

Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Jihar Kano Ta Dauki Matakin Ladabtarwa aKan Alkalin da Ya Yi Sakaci a ayyukansa.

Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Jihar Kano (JSC), ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Justice Dije Abdu Aboki, ta ɗauki matakan ladabtarwa a zaman ta na 88 da aka gudanar ranar 1 ga Disamba, 2025.

A cewar wata sanarwa da memagana da yawun Ma’aikatar Shari’a, Baba Jibo Ibrahim, ya fitar, hukumar tai duba tare da amincewa da rahoton kwamitin Judiciary Public Complaint Committee (JPCC), wanda ya gudanar da bincike kan wasu ƙorafe-ƙorafe da aka shigar akan wasu jami’an shari’a.

Daga cikin matakan da aka ɗauka, an samu Alkalin Babban Kotun Shari’a na Dambatta, Umar Bala Musa, da laifin jinkirta fitar da bayanan shari’a fiye da lokacin da kundin tsarin mulki ya tanada  wato kwana bakwai. Duk da an yi masa roƙo sau da dama na tsawon watanni uku, amma bai cika wannan sharadi ba.

A saboda haka, hukumar ta ba shi gargaɗi irin  na hukuma tare da umartarsa da ya bi doka da ƙa’idar aikin shari’a yadda ya kamata a gaba.

JSC ta sake jaddada kudurinta na tabbatar da gaskiya, amana da kare hakkin jama’a a harkokin shari’a. Haka zalika hukumar tana mai tabbatar da cewa ba za ta lamunci wani nau’i na rashin gaskiya ko sakaci daga jami’anta ba.

Baba Comrade, E-Magazine

Justice dije
Justice dije

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version