eMagazine Media Channel Education Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu domin hutun Ramadan da Karamar Sallah
Education Uncategorized

Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu domin hutun Ramadan da Karamar Sallah

IMG 20260225 WA0002

IMG 20260225 WA0002

Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu domin hutun Ramadan da Karamar Sallah

Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa za a rufe dukkanin makarantun firamare da sakandare, na gwamnati da masu zaman kansu, a ranar Asabar 1 ga Maris, 2026, domin fara hutun Azumin Ramadan da na Karamar Sallah.

Sanarwar ta bayyana cewa wannan mataki ya yi daidai da jadawalin shekarar karatu ta 2025/2026 da aka amince da shi, inda hutun zai shafi dalibai masu kwana a makaranta da na rana baki daya.

Gwamnatin ta bukaci iyaye da masu kula da daliban da ke makarantun kwana da su je su dauki ‘ya’yansu tun daga safiyar ranar Juma’a 30 ga Fabrairu, 2026.

A cewar sanarwar, daliban makarantun kwana za su koma makaranta ranar Lahadi 22 ga Maris, 2026, yayin da daliban rana za su koma ranar Litinin 23 ga Maris, 2026.

Haka kuma, an bayyana cewa zangon karatu na biyu zai ci gaba daga ranar Lahadi 22 ga Maris, 2026, kuma zai kare a ranar Asabar 18 ga Afrilu, 2026.

Ali Haruna Abubakar Makoda, Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, ya yi kira ga iyaye da masu kula da dalibai da su tabbatar da cewa an bi ranakun komawa makaranta kamar yadda aka tsara.

Gwamnatin ta kuma umurci dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da su bi wannan tsari, tare da gargadin cewa duk wata makaranta da ta sabawa umarnin za a dauki mataki a kanta.

A karshe, gwamnatin ta gode wa iyaye da al’ummar jihar bisa hadin kai da goyon bayan da suke bai wa Ma’aikatar Ilimi, tare da yi wa dalibai fatan kammala azumin Ramadan cikin nasara da gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version