News

GWAMNATIN KANO TA JAJANTA WA IYALAN WADANDA SUKA RASA RAYUKA A HARIN EDO, TA BA SU TALLAFI

IMG 20260323 WA0016
IMG 20260323 WA0016

GWAMNATIN KANO TA JAJANTA WA IYALAN WADANDA SUKA RASA RAYUKA A HARIN EDO, TA BA SU TALLAFI

Daga Wakilinmu

Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jagoranci wata tawaga ta gwamnatin jihar zuwa Fadar Mai Girma Hakimin Bunkure domin jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wani hari da ya faru a Jihar Edo a bara.

 

A cewarsa, wannan lamari mai matukar raɗaɗi ya afku ne yayin da mamatan ke kan hanyarsu ta dawowa gida domin gudanar da bukukuwan Sallah, lamarin da ya kara jefa iyalansu cikin alhini da jimami.

 

Yayin ziyarar, Kwamishinan ya isar da sakon ta’aziyya da jajircewar Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, wanda ya bayyana cewa har yanzu gwamnati na tare da iyalan mamatan a wannan lokaci na jarrabawa.

 

A cewarsa, “Mai Girma Gwamna yana matukar tausaya wa iyalan da abin ya shafa, kuma yana tabbatar musu da cewa gwamnati ba za ta manta da su ba.”

 

Ya kara da cewa, a matsayin wani bangare na rage radadin halin da iyalan ke ciki, Gwamnan ya amince da bayar da tallafin kudi da kayan abinci ga wadanda abin ya shafa.

 

A cewar Kwamared Waiya, iyalan mutane 16 da suka rasu sun karbi Naira 300,000 kowannensu, yayin da mutane 13 da suka jikkata suka samu Naira 200,000 kowannensu. Haka kuma, an rabawa kowane daga cikinsu buhunan shinkafa guda biyu.

 

Bugu da kari, ya tabbatar wa iyalan cewa gwamnatin Jihar Kano na ci gaba da tuntubar gwamnatin Jihar Edo domin tabbatar da cewa an biya su diyya yadda ya dace.

 

Kwamishinan ya yi kira ga iyalan da su ci gaba da nuna hakuri da juriya, yana mai jaddada cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da kula da su har zuwa lokacin da za su samu hakkokinsu na diyya, da ikon Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *