GWAMNATIN KANO TA HARAMTA SAYAR DA FILAYEN MAKARANTU,ASIBITI DA DUK WANI WAJE MALLAKIN GWAMNATI
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da haramta duk wani nau’in mu’amalar filaye da suka shafi makarantu, asibitoci da sauran kadarorin gwamnati a faɗin jihar, tare da jaddada aniyarta na kare kadarorin jama’a da kuma dawo da daidaito a harkokin gudanar da filaye.
An bayyana hakan ne ta bakin Kwamishinan Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsaren Birane, Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar, yayin wata ziyara da ya kai Makarantar Government Girls’ College Kano,(tsohuwar Women Teachers College), sakamakon rahotannin da ke nuna an mamaye wani babban ɓangare na filin makarantar ba bisa ƙa’ida ba.
A cewar Kwamishinan, an gudanar da wannan bincike ne bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf bayan samun rahotannin cewa wasu mutane sun shiga harabar makarantar ba tare da izini ba, tare da fara raba filaye domin gina gidajen zama na kashin kai.
Ya bayyana cewa nan take Gwamnan ya umarci Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsaren Birane da ta dakatar da duk wani aiki da ake yi a wurin tare da gudanar da cikakken bincike kan yadda aka yi zargin raba filayen.
Hon. Abduljabbar ya bayyana cewa binciken farko ya nuna an riga an ware kusan filaye 100 a cikin harabar makarantar domin gina gidajen zama na masu zaman kansu.
Ya bayyana wannan lamari a matsayin babbar barazana ga ɓangaren ilimi na jihar, yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na sauya kadarorin gwamnati da aka ware domin ilimi da sauran ayyukan jama’a zuwa mallakar masu zaman kansu ba.
Kwamishinan ya yi gargaɗin cewa duk wani mutum ko kamfanin gine-gine da ya saɓa wa wannan umarni zai fuskanci hukuncin doka, yana mai cewa ma’aikatar za ta tabbatar da aiwatar da duk dokokin da suka dace domin hana sake faruwar irin wannan take doka.
Haka kuma, ya sanar da cewa daga ranar 3 ga Agusta, 2026, dukkan filayen da ke mallakar makarantu, asibitoci da sauran cibiyoyin gwamnati a faɗin Jihar Kano sun koma ƙarƙashin kulawa da gudanarwar Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsaren Birane a madadin Gwamnatin Jihar Kano.
Ya ƙara da cewa saboda haka, gwamnati ta haramta gaba ɗaya rabon filaye, bayar da su, sayarwa, canja mallaka ko sauya amfaninsu idan suna cikin makarantu, asibitoci ko sauran cibiyoyin gwamnati a ko’ina cikin Jihar Kano.
Hon. Abduljabbar ya kuma yi kira ga al’ummar ƙananan hukumomi 44 na jihar da su mara wa gwamnati baya ta hanyar kai rahoton duk wani mamaye fili ba bisa ƙa’ida ba, ƙwace filaye ko gine-ginen da aka yi ba tare da izini ba ga hukumomin gwamnati da suka dace ko kuma ta kafafen yaɗa labarai.
Da take jawabi yayin ziyarar, Shugabar Makarantar Government Girls Secondary School, Goron Dutse, Uwani Ahmad Balarabe, ta yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwamishinan Filaye bisa saurin ɗaukar matakin magance matsalar mamaye filin makarantar.
Ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici da kuma wanda ba a taɓa fuskanta ba, tana mai tunawa cewa a tsawon sama da shekaru talatin da ta shafe tana aiki a makarantar, an kasance cikin yanayi na lumana da ingantaccen muhalli na koyarwa da koyo.
Shugabar makarantar ta nuna damuwarta cewa mamaye filin ba bisa ƙa’ida ba ya cinye wani babban ɓangare na filin makarantar, lamarin da ke barazana ga faɗaɗa ta da ci gabanta a nan gaba.
Ta bayyana ƙwarin gwiwarta cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta ɗauki matakan da suka dace domin ƙwato filin makarantar tare da kare martabar ta da gadonta na ilimi domin amfanin al’ummomi masu zuwa.
