Gwamna Abba Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Haruna Bashir
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar ta’aziyya ga Malam Haruna Bashir, wanda aka kashe masa dukkan iyalansa a unguwar Chiranci.

A ranar Laraba, 21/1/2026, Maigirma Gwamnan Jahar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da tawagarsa, ya ziyarci Malam Haruna Bashir domin jajanta masa da nuna alhininsa kan mummunan lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar matarsa da ‘ya’yansa guda shida. Gwamnan ya kai ziyarar ne a gidansu da ke Kofar Nassarawa.
Gwamna Abba ya bayyana matuƙar alhininsa da damuwarsa kan wannan mummunan aiki na rashin imani da aka aikata wa iyalan Malam Haruna. Gwamnan ya yi masa wasu alƙawura, inda ya ce, Gwamnatin Jihar Kano za ta ɗauki nauyin kuɗin tikitinsa, guzuri da kuma wajen zamansa a ƙasar Saudiyya, bayan wani bawan Allah ya riga ya biya masa kuɗin Umrah. Haka zalika, Gwamnan ya bayyana cewa, gwamnati za ta biya masa kuɗin kujerar aikin Hajjin shekarar 2026.
Bugu da ƙari, Gwamnan ya ce , gwamnati za ta rushe gidan Malam Haruna Bashir da ke Chiranci domin mayar da shi masallaci, tare da ba shi wani gida a wurin da ya dace a matsayin tallafi. Gwamna Abba ya shawarci Malam Haruna Bashir da ya dogara ga Allah, ya yi haƙuri, sannan ya sa ran samun wata matar aure a nan gaba wadda za ta rage masa kewa, inda ya tabbatar masa cewa gwamnati za ta ɗauki nauyin aurennasa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su kasance masu sa ido, tare da gaggauta kai ɗauki duk lokacin da suka ji ihu ko kiran taimako da ba a saba ji ba, yana mai jaddada cewa hakan hakki ne a kansu.
Gwamna Yusuf ya ce da zarar kotu ta kammala aikinta, gwamnati za ta tabbatar da an aiwatar da hukunci cikin gaggawa bisa adalci.
Baba Comrade, E-magazine
21/1/2026