Security

DOKAR HANA GOYO AKAN BABURA MASU ƘAFA BIYU IYA MASU SANA’AR ACAƁA TA SHAFA KAWAI

1764960150895
1764960150895

Kwamishinan Shari’a na jahar Kano Barrister Abdulkarim ya yi ƙarin haske akan dambarwar da aka samu jahar Kano bayan hukumar Yansanda su ka sanar da dokar nan ta hana goyon biyu akan babura masu ƙafa biyu.

Kwamishinan Shari’a ya sanar da manema labarai. A inda ya ce , ita wannan doka ta hana goyon biyu akan babura ta ta’allaka ne ga masu yin sana’ar Acaɓa kawai. Dan haka duk wanda ya san ba acaɓa ya ke yi da Babur dinsa to zai iya goyan iyalansa ko wasu mutane, amma ba da zumman sana’a irin ta acaɓa ba.

Ga yadda hirar tamu ta kasance da Kwamishinan Shari’a na jahar Kano.

Baba Comrade, E-Magazine

05/12/2025

https://www.facebook.com/share/v/1Cy7Azhjwf/

1764960150895
KWAMISHINAN SHARI’A

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *