Budaddiyar Wasika Zuwa ga Gwamnan Kano da Grandi Khadi akan Alƙalin Hukumar Hisba Sani Tanimu
Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu
Ya mai girma gwamnan Kano mai adalci Alh Abba Kabir Yusuf da shugaban alkalan kotunan shari’ar Musulunci na jihar kano Dr Tijjani Yusuf Yakasai ina muku fatan alheri Allah ya kara muku lafiya da kwanciyar hankali ameen.
Maigirma Gwamna da Grandi Khadi na rubuta wannan takardar ne akan alkalin Hukumar Hisba Sani Tanimu kan rashin adalci da yake yi a aikin sa, tare da nuna son zuciya da bangaranci yayin gabatar da Shari’a kamar yadda mahaifiyar wata yarinya tayi mana korafi.
Akwai wasu yara mata da suka yi rikici tsakaninsu, har suka fada ruwan zafi, hakan ya janyo wadda tafi konewar matar aure ce zata kai shekara 20 ko kusa da haka, abokiyar fadan kuma zata kai shekaru 17, hakan ya janyo har Police station aka kai case din, mijin matar da iyayenta suka hakura amma, wani fitinnen tsohon Alkali maisuna Idris Yahya ana masa laƙabi da Mai Hannu Ɗaya dan unguwar Sheka wanda yake a matsayin sirikin mijin yarinyar yace bai hakura ba, saboda wasu dalilai nasa! Haka aka ajiye yarinyar nan ta kwana a tsare, washe gari aka kaita Kotun hisba, wanda Kafin aje shi wannan tsohon alkalin maihannu ɗaya wato Idris Yahya ya shirya da an je a daure yarinyar saboda yana da alaƙa da alkalin.
Ana zuwa kuwa shi Alkalin Hisba ya tura yarinyar gidan gyaran hali zuwa tun ranar Alhamis sai ranar Litinin, anyi anyi a bada beli duba da ƙarancin shekarunta da kuma cewar fada suka yi tare, amma ya kekasa kasa yaƙi duk don farantawa shi wannan tsohon alkalin saboda maigidansa ne.
Da aka dawo ranar Litinin sai kotu ta ɗaga shari’ar har sallah Babba ya sake mai da yarinyar nan gidan gyaran hali sai da ta kara kwana 11 a rufe, sai jumaat 5 ga wata aka bada belin ta da kyar
Don haka ne maigirma gwamna da grandi Khadi Mahaifiyar wannan yarinyar ta ce bata da wani gata sai Allah sai ku, tace bata da hanyar ganinku, amma jaridar Alfijir ta sanar da ku domin a nema wa yarinyarta hakkin wannan cin zarafin da tsohon alkalin Idris Yahya ya saka Alkalin Hisba Sani Tanimu yayi musu.
Ina muku fatan alheri Allah ya sa a gama lafiya.
Editan Jaridar Alfijir Labarai

