AOPSHON ta jahar Kano ta Haramta duk wani taron Shugabannin Makarantu ba tare da Izinin shugabanta na Jihar Kano ba
Ƙungiyar Shugabannin Makarantun Firamare ta Nijeriya (AOPSHON), reshen Jihar Kano, ta sanar da haramta duk wani taron shugabannin makarantu da ake gudanarwa ba tare da samun amincewar Shugabanta na Jiha ba.
Shugaban AOPSHON na Jihar Kano, ya bayyana hakan yayin da yake nesanta ƙungiyar daga wani taro da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Gwale. Ya ce ƙungiyar ba ta ba da izinin gudanar da taron ba, don haka ba ta amince da duk wani sakamako da ya fito daga cikinsa ba.
Kwamared Sumaila ya jaddada cewa daga yanzu, AOPSHON a Jihar Kano ba za ta lamunci duk wani mutum ko ƙungiya da ke shirya taruka a ƙananan hukumomi da nufin tayar da hankali ko rikici tsakanin shugabannin makarantu da malamai ba. Ya kuma ƙara da cewa, har ma shugabannin rassan ƙananan hukumomi dole ne su nemi izini kafin su kira kowane irin taro.
Ya yi gargadin cewa, za a ɗauki matakan ladabtarwa kan duk wani mamba da ya karya wannan doka.
Shugaban ya kuma sake jaddada kudirin ƙungiyar na kare haɗin kai da mutuncinta, yana mai cewa ba za a ƙara bari wani mutum ya ke yi wa ƙungiyar zagon ƙasa ba.
AOPSHON na kira ga dukkan shugabannin makarantu a faɗin ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano da su ƙaurace wa duk wani taro da ya saɓa da kundin tsarin mulkin ƙungiyar.
Sanarwa daga:
Kwamared Bilkisu T. Abdulkadir
Sakatariya ta
AOPSHON, Reshen Jihar Kano

