eMagazine Media Channel News AN KADDAMAR DA YFPM A AREWACIN NIGERIA
News

AN KADDAMAR DA YFPM A AREWACIN NIGERIA

IMG 20260209 WA0006

IMG 20260209 WA0006

An Kaddamar da YFPM a Arewacin Najeriya, An Yi Kira da Ƙara Shigar Mata a Harkar Kafofin Watsa Labarai

Ƙungiyar Young Female Professionals in Media (YFPM) ta kaddamar da mambobinta da kwamitin zartarwa a birnin Kano, arewacin Najeriya, da nufin ƙarfafa shigar mata da jagorancinsu a masana’antar kafofin watsa labarai ta ƙasa.

An gudanar da bikin kaddamarwar a ranar 7 ga Fabrairu, 2026 a Tahir Guest Hall da ke jihar Kano, inda aka tattaro ’yan jarida, malamai, jami’an gwamnati da matasan mata masu aikin kafafen watsa labarai domin tattauna ƙwarewa, ɗabi’a da shigar mata cikin aikin jarida.

A jawabin buɗe taron, shugabar YFPM, Maryam Usman Nagado, ta bayyana cewa an kafa wannan dandali ne domin tallafa wa matasan mata a fannin kafofin watsa labarai ta hanyar shiriya (mentorship), bunƙasa ƙwarewa da haɗa kai, tare da magance tsoffin ƙalubalen da ke hana mata samun ci gaba a fannin.

Babban sakataren yaɗa labarai na gwamnatin jihar Kano, Mustapha Muhammad, ya jaddada muhimmancin aikin jarida.  Ya shawarci matasan mata masu sana’ar watsa labarai da su kasance jajirtattu tare da dagewa kan bin ƙa’idojin sana’a.

Farfesah Hadiza Ibrahim ta bayyana ƙalubalen tsari da al’adu da mata ke fuskanta a harkar kafofin watsa labarai, tana mai cewa dogaro da kai, ƙarfin tunani da ci gaba da koyo su ne muhimman ginshiƙai ga mata masu neman matsayi na jagoranci a aikin jarida.

Dakta Bala Muhammad, ya yi kira ga ’yan jarida da su riƙe gaskiya da amana tare da rungumar sababbin dabaru, la’akari da saurin sauyin yanayin kafofin watsa labarai na duniya.

Daya daga cikin muhimman lokutan taron shi ne ƙaddamar da Kalanda ta YFPM da Arc. Ahmad Abba Yusuf, Sakataren Zartarwa na Hukumar Tarihi da Al’adu ta Jihar Kano. Bayan kaddamarwar, mahalarta taron sun bayar da gudummawar kuɗi, alamar ƙara samun goyon bayan hukumomi ga manufofin ƙungiyar.

Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce, kafa YFPM a Arewacin Najeriya abu ne da yazo a lokacin da ya dace.  Ƙara yawan mata a jagorancin kafafen watsa labarai yana da matuƙar muhimmanci wajen samar da tattaunawar jama’a da samar da haɗin kai. Ya kuma tabbatar da goyon bayan gwamnatin jahar Kano ga wannan shiri.

An kaddamar da mambobin ƙungiyar tare da rantsar da su a hukumance ta hannun lauya Badiha Abdullahi Muaz, wadda ta yi musu nasiha da su kiyaye kundin tsarin ƙungiyar da ƙa’idojin ɗabi’a.

Wakilai daga Ƙungiyar Mata ’Yan Jarida ta Najeriya (NAWOJ) da Hukumar Kwastam ta Najeriya su ma sun yi jawabi, inda suka yi kira da a ƙara ƙwarewa da haɗin guiwa mai ƙarfi tsakanin kafofin watsa labarai da hukumomin gwamnati.

Kaddamar da YFPM na nuna fara wani tsari na haɗin guiwa domin ɗaga martaba, tasiri da jagorancin matasan mata a fannin kafofin watsa labarai na Najeriya.

Duk mai son a yi masa talla ko yada wani labari za a iya nemanmu ta lambar waya: 08036614747 ,  09125443108

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version