ILIMI YA INGANTA A GWALE, MAKARANTU SUN HAU SAITI
Hukumar Ilimi ta Karamar Hukumar Gwale (LGEA) ta samu gagarumin ci gaba a fannin koyarwa da ilmantarwa a makarantunta, sakamakon cikakken aikin sa ido, tantancewa, da tabbatar da ingancin ilimi da aka gudanar a zangon karatu na shekarar 2025/2026.
Shugabar Sashen Tabbatar da Inganci, Malama Furaira Muhammad, ta danganta wannan nasara da ci gaba da kokarin tabbatar da bin ka’idojin ilimi da kuma inganta hanyoyin koyarwa a makarantu.
Ta bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da Sashen Hulɗa da Jama’a na LGEA ta Gwale, inda ta jaddada cewa an samu ingantuwar auna inganci a fannin koyarwa, yanayin makarantu, da kuma tafiyar da harkokin gudanarwa a yawancin makarantu.
Furaira ta kara da cewa, tabbatar da inganci na nufin sa ido da tantancewa na tsari domin tabbatar da cewa malamai da hanyoyin koyarwa sun cika ka’idojin da ake bukata. Ta ce babban burin hakan shi ne samar da ingantaccen ilimi da zai amfani dalibai da al’umma baki daya.
Sai dai ta nuna akwai bukatar kara inganta wasu fannoni, musamman wajen amfani da kayan koyarwa da koyo, karfafa tsarin tsara ci gaban makarantu (SSE/SDP), da kuma tabbatar da samar da tsaftataccen ruwan sha da ingantattun hanyoyin tsafta a makarantu. Ta kuma yaba wa jami’an da ke taimakawa sashen bisa jajircewarsu da hadin kai wajen tabbatar da nasarar ayyukan sashen.
A nasa jawabin, Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar Gwale, Kwamared Muntari Inuwa, ya yabawa sashen bisa kokari da sadaukarwa, yana mai cewa ana kara kaimi wajen tabbatar da samar da ingantaccen ilimi ga dukkan dalibai.
Ya kuma yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su hada kai domin kara bunkasa fannin ilimi a Gwale.
Sanya hannu:
Safiya Muhammad Hamza
Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Kamfani
Gwale LGEA
