APC Ta Fitar da Jadawalin Zaɓen 2027, Ta kuma fitar da farashin kuɗin Fom ɗin Takara
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fitar da jadawalin lokuta da tsarin ayyukan da za a bi domin gudanar da Zaɓen Shekarar 2027.
Wannan na kunshe ne a cikin jadawalin ayyukan da Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa na jam’iyyar, Sulaiman Muhammad Argungu, ya sanya wa hannu.
Jadawalin ya bayyana lokutan tantance ‘yan takara, sauraron ƙorafe-ƙorafe, da gudanar da zaɓen fidda gwani, tare da umarni kan sayar da fom ɗin nuna sha’awa da na tsayawa takara.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “APC na tabbatar wa ‘ya’yanta, masu ruwa da tsaki da ‘yan Najeriya cewa za ta gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani cikin gaskiya da adalci, wanda zai ƙara ƙarfafa dimokuraɗiyyar cikin gida da kuma manufofin jam’iyyar na ci gaba.”
A cewar jadawalin, sayar da fom zai fara daga ranar Asabar, 25 ga Afrilu, kuma zai ƙare ranar Litinin, 4 ga Mayu, 2026.
An nuna cewa zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa zai gudana tsakanin 15 zuwa 16 ga Mayu; na Majalisar Wakilai a ranar 18 ga Mayu; na Majalisar Dattawa a ranar 20 ga Mayu; na Majalisar Dokokin Jihohi a ranar 21 ga Mayu; yayin da na gwamna zai gudana a ranar 23 ga Mayu, 2026.
Haka kuma, jadawalin ya nuna cewa sauraron ƙorafe-ƙorafe na zaɓen shugaban ƙasa zai gudana a ranar 18 ga Mayu; na Majalisar Wakilai a ranar 20 ga Mayu; na Majalisar Dattawa a ranar 21 ga Mayu; na Majalisar Dokokin Jihohi a ranar 23 ga Mayu; sannan na gwamna a ranar 25 ga Mayu, 2026.
Jam’iyyar ta kayyade farashin fom ɗin nuna sha’awa ga masu neman takarar shugaban ƙasa a kan naira miliyan 30, yayin da fom ɗin tsayawa takara yake naira miliyan 70. Ga masu neman takarar gwamna, fom ɗin nuna sha’awa naira miliyan 10 ne, yayin da na tsayawa takara yake naira miliyan 40.
Haka kuma, ga Majalisar Dattawa, fom ɗin nuna sha’awa naira miliyan 3 ne, yayin da na tsayawa takara yake naira miliyan 17. Ga Majalisar Wakilai, fom ɗin nuna sha’awa naira miliyan 1 ne, yayin da na tsayawa takara yake naira miliyan 9. Ga Majalisar Dokokin Jihohi kuwa, fom ɗin nuna sha’awa naira miliyan 1 ne, yayin da na tsayawa takara yake naira miliyan 5.
An kuma bayyana cewa mata, matasa da masu nakasa za su biya kudin fom ɗin nuna sha’awa kawai tare da rabin (50%) na kuɗin fom ɗin tsayawa takara da aka kayyade.
Domin neman karin bayani, ko talla ko isar da sako za ku iya kiranmu ta kan wannan lambar wayar 08036614747
