Education

NUT TA FARA BIYA WA MALAMAN SA KAI KUDIN KARATU

IMG 20260202 WA0008
IMG 20260202 WA0008

NUT TA KURA TA ƊAUKI NAUYIN BIYA WA MALAMAN SA KAI KUDIN KARO KARATU NA GABA DANA SECONDARY.

Ƙungiyar Malaman makaranta ta Najeriya (NUT) reshen karamar hukumar Kura ta ɗauki nauyin biya wa wasu zakakuran malaman makaranta masu koyarwa kyauta a makarantun dake karamar hukumar Kura.

IMG 20260202 WA0009

Shugaban ƙungiyar Comrade Abubakar Kura ya ce, ‘ mun ɗauki nauyin biya wa duk wani malami da ya ke bada lokacinsa Wajan koyar da daliban Kura kyauta, wanda a wannan rana ta Litinin mu ka biya wa ɗaya daga cikin malaman voluntary kuɗin fara karatun NCE mai suna Asiya Surajo Sani.’ Kura ya ce , kungiyar NUT za ta ci gaba da biya wa kowanne voluntary teacher kuɗin karatu har ya gama karatunsa matukar ya ci gaba da koyar da daliban Kura kyauta.

Asiya Surajo Sani ta ce, ita Malama ce da ta ke koyarwa a makarantar Ihya’ussunnah Islamiyya Primary School Kura kusan tsahon shekaru uku . Asiya ta yi godiya sosai ga shugaban ƙungiyar NUT ta Kura

Iliyasu Kura, NUT Kura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *