Uncategorized

MAKOMAR SUFURIN KANO: MASU RA’AYI SUN NEMI A KOMA MOTOCIN LANTARKI DA RANAR SOLA

1766693606478
1766693606478

MAKOMAR SUFURIN KANO: MASU RA’AYI SUN NEMI A KOMA AMFANI DA ABABAN HAWA MASU AMFANI DA LANTARKI DA SOLA

Tattaunawa kan dorewar tsarin sufuri a Jihar Kano ta samu gagarumin mahimmanci a ranar Litinin, 15 ga Disamba, 2025, yayin da masu ruwa da tsaki suka hallara a taron tattaunawa na kwana ɗaya kan tsarin CNG (Compressed Natural Gas), motocin da ba sa fitar hayaki (soot-free buses), da manufofin ababan hawa masu amfani da lantarki (EV), wanda Ƙungiyar Africa Health Budget Network (AHBN) ta shirya. Taron da aka gudanar a ginin AHBN, No. 9 Kura Road, Off Lamido Crescent, Nassarawa GRA, an shirya shi ne don tattara ra’ayoyi kan irin shirin da Kano ke da shi wajen aiwatar da sabbin dokokin sufuri na ƙasa, tare da la’akari da rawar da hukumomin jihar Kano ta ke takawa . Da kuma ƙungiyoyin fararen hula, dana  ‘yan jarida, da masu harkar sufuri za su taka wajen samar da tsarin sufuri mai tsafta da inganci.

Daya daga cikin mahalarta tattaunawar, Tijjani Sarki, masani a kan kyakkyawan shugabanci da manufofin jama’a, ya bayyana ra’ayinsa mai cike da yabawa da kuma gargadi.

Yayin da yake yaba wa shirin gwamnatin tarayya na Presidential Initiative on CNG (PICNG), Sarki ya bayyana fa’idodin tattalin arziki da ke tattare da shirin, ciki har da rage farashin mai da samar da ayyukan yi. Sai dai ya ja kunnen mahalarta kan illa da amfani da CNG ka iya yi wa muhalli, yana mai cewa wajibi ne a fara shirin sauya zuwa motocin da ke amfani da lantarki da rana (solar), domin cimma manufofin kare muhalli.

Sarki ya ƙara da cewa “Ko da yake CNG yana da alfanu, ba za mu iya watsi da barazanar da ke tattare da shi ga muhalli ba. Kano ya kamata ta fara shirin komawa ga Motocin Lantarki da Sola domin bin sahun ci gaban duniya,”

Ya kuma haskaka wasu manyan ƙalubale da ake fuskanta a tsarin sufuri na Jihar Kano:

1- Rashin wadatattun cibiyoyin sauya motocin zuwa amfani da CNG da kuma wuraren cika iskar, yana hana sauƙin amfani da wannan tsari.

2- Yawancin titunan jihar sun gaji ko kuma basu da inganci, ba su da wadatattun wajan tsayawar motoci (bus stops), babu tashoshin sauka da hawa, babu layin masu tafiya a ƙasa, da kuma layin da aka ware wa babura da ƙeke napep (adaidaita sahu).

Zama da ƙeke napep a manyan tituna na jihar na janyo cunkoso, wanda ya sa Sarki ya ba da shawarar a takaita zirga-zirgarsu zuwa wasu hanyoyi na daban, tare da bada fifiko ga manyan tituna kamar BUK Road, MM Road, IBB Road, Ibrahim Taiwo Road, Katsina, Hadejia da Maiduguri Road don motocin CNG da na lantarki (EV).

Sannan kuma ya bayyana bukatar kafa tsarin Bus Rapid Transit (BRT) mai inganci don sauƙaƙa cunkoso da inganta tafiyar fasinja.

Sarki ya kuma nuna damuwa kan rashin da’a da gini ba tare da izini ba a kan manyan tituna, yana kiran da a ƙarfafa doka da bin ƙa’idojin tsara birane. Ya jaddada bukatar ƙwarewar gudanar da ayyukan KAROTA da kuma ɗaukar karin jami’an kula da zirga-zirga domin tabbatar da tsaro da oda a tituna.

A ƙarshe, ya yi kira mai ƙarfi da a ɗauki mataki ta hanyar tsara manufofi, wayar da kai ga jama’a, da shirin dogon lokaci. Ya buƙaci gwamnati da al’umma su rungumi hanyoyin sufuri masu dorewa da za su kare muhalli tare da habaka tattalin arzikin Kano.

Sarki ya ce “Makomar sufuri tana cikin ababan hawa masu aiki da lantarki kuma masu amfani da hasken rana. Kuma yanzu ya kamata a ɗauki mataki ,”

Tijjani Sarki

Mai rajin Kyakkyawan Shugabanci da Tsare-tsaren Jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *