Kungiyar malaman makaranta reshen karamar hukumar Gaya ta kai ziyarar dubiya ga wasu malaman makaranta a ranar Lahadi 7/12/2025.
Shugaban kungiyar NUT na karamar hukumar Gaya Comrade Gaya tare da mataimakansa ne su ka shirya wannan ziyarar dubiya da jaje ga wasu daga cikin malaman makaranta waɗanda su ka haɗa da malam Isah Idi Kademi tare da bashi tallafin kuɗin magani. Comrade Gaya ya ce , mun kai wannan Ziyarar ne ga marasa lafiya domin jajanta musu da kuma basu tallafin kuɗaɗen shan magani da kuma yi musu addu’a .
Comrade Gaya ya ƙara da ce wa, kowanne majinyaci da mu ka je duba shi mun bashi tallafin kuɗi.
