’Yantakarar ADP sun yi ta’aziyyar rasuwar Alhaji Sani Ayagi
KANO, JUMA’A, 9 GA OKTOBA, 2026
Ɗan takarar jam’iyyar ADP mai neman kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar mazaɓar Gwale, Hon. Dr. Bashir Aliyu Hausawa, tare da abokin tafiyarsa na siyasa, Hon. Amb. Ja’afar Adam, sun miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Sani Ayagi a unguwar Tal’udu da ke Kano.
A lokacin ta’aziyyar, ’yansiyasar sun yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙan marigayin, Ya gafarta masa kura-kuransa da zunubansa tare da neman Allah ya yi masa rahama, sannan Ya sa ya kasance cikin waɗanda za su sami kusanci da Annabi Muhammad (SAW) a Aljannatul Firdausi.
Sa hannu:
Hon. Dr. Bashir Aliyu Hausawa da Hon. Amb. Ja’afar Adam

