YAKI YA BARKE A GABAS TA TSAKIYA: IRAN TA MAYAR DA MARTANI AKAN SANSANIN SOJAN AMURKA, TASIRI YA YADU A YANKIN
Tashin hankali ya kara kamari a Gabas ta Tsakiya bayan awa guda kacal da harin hadin gwiwa na Amurka da Isra’ila kan Iran, inda Tehran ta mayar da martani cikin gaggawa ta hanyar kai hare-hare kan Isra’ila da kuma kadarorin sojin Amurka da ke kasashen Qatar, Bahrain, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Kuwait, Jordan da Saudiyya.
Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki na farko da Iran ta dauka ya nuna yiwuwar kuskuren lissafi a bangaren Washington da Tel Aviv, musamman ganin yadda martanin ya zo cikin sauri ba tare da jinkiri ba. Masu nazari na ganin cewa tasirin wannan sabon rikici na fara bayyana a yankin, lamarin da ka iya haifar da karin dagulewar al’amura a fannin tsaro da siyasa.
Gaggawar mayar da martanin daga Tehran ta nuna cewa ba a samu shammatar Iran ba, sabanin yadda aka sha gani a wasu rikice-rikicen baya. Duk da rahotannin cewa Amurka da Isra’ila sun gudanar da bincike da tattara bayanan leken asiri kafin kai harin, martanin Iran ya ba da mamaki ga masu lura da al’amuran tsaro.
Haka kuma, shugabannin Iran sun bayyana cewa rikicin ba zai takaita ga dan lokaci ba, suna nuni da yiwuwar tsawaita rikicin idan har hare-haren suka ci gaba. Wannan furuci na kara jaddada fargabar cewa Amurka na iya tsunduma cikin wani dogon rikici mai sarkakiya, wanda fita daga cikinsa zai iya zama kalubale fiye da yadda aka zata.
A gefe guda, Amurka ta dogara da tsarin makami mai kakkabo makamai na THAAD da ta girke a Isra’ila da kuma wasu sansanoninta da ke yankin, da nufin dakile duk wani hari daga Iran. Sai dai matakin da Tehran ta dauka ya nuna cewa sabuwar fuskantar barazana na bukatar karin lissafi da dabaru a bangaren tsaro.
Masu sharhi na ci gaba da bibiyar yadda al’amuran za su kaya a cikin kwanaki masu zuwa, yayin da kasashen yankin ke cikin shirin ko-ta-kwana domin kare muradunsu da tsaron al’ummominsu.

