VCT Forum Ta Bukaci Gwamnatin Kano Ta Inganta Albashin Malaman Makaranta, Kamar Yadda Ta Yi wa Ma’aikatan Lafiya dana Higher Education
Ƙungiyar ta ce malaman makaranta sun cancanci ingantaccen albashi da kyakkyawan yanayin aiki, tare da kira ga NUT da NLC da su tabbatar da adalci da bai wa kowa dama a harkokin ƙungiyoyi.
Ƙungiyar Voice Concerned of Teachers (VCT Forum) ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta inganta albashi da yanayin aikin malaman makarantu, kamar yadda aka bayyana cewa ana ƙoƙarin daidaita albashin ma’aikatan lafiya da na ma’aikatan manyan makarantun ilimi.
Shugaban ƙungiyar, Comrade Abbas Adamu, ya bayyana cewa matsalolin da malaman makarantun firamare ke fuskanta sun wuce batun daidaita albashinsu da na sauran ma’aikatan gwamnati kawai.
A cewarsa, halin da malamai suke ciki yana nuna akwai buƙatar ƙara ba ilimi da waɗanda suke koyarwa muhimmanci, tare da inganta walwalarsu da yanayin aikinsu.
Ya jaddada cewa malaman Kano sun cancanci samun albashin da zai yi gogayya da na takwarorinsu na sauran jihohi, ciki har da Adamawa da Jigawa, waɗanda a cewarsa ba su kai Kano ƙarfin tattalin arziki ba.
Comrade Abbas ya bayyana jin daɗinsa kan rahotannin cewa Gwamnatin Jihar Kano na shirin daidaita albashin ma’aikatan lafiya na jihar da na takwarorinsu na gwamnatin tarayya, inda ya bayyana matakin a matsayin abin a yaba.
Sai dai ya bayyana cewa malaman makarantu ma sun cancanci irin wannan kulawa, yana mai cewa su ne tushen gina dukkan sauran sana’o’i da ƙwarewar da ake buƙata wajen ci gaban al’umma.
Ya ce:
“Mun yi imanin cewa malamai sun cancanci kulawa ta musamman, domin mu ne tushen da ake gina sauran sana’o’i a kai. Haka kuma, malamai suna fuskantar matsin tattalin arziki da wahalhalun rayuwa, tare da ƙalubalen aikin koyarwa da ke buƙatar haƙuri da jajircewa.”
Shugaban VCT Forum ya kuma yi kira ga Ƙungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT) da Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) da su fahimci muhimmancin gudummawar malamai, tare da tabbatar da cewa ana ba da kulawa mai kyau ga walwalarsu.
Bugu da ƙari, ya buƙaci waɗannan ƙungiyoyin ƙwadago da su rungumi tsarin shugabanci mai bai wa kowa dama, ta yadda dukkan mambobinsu za su samu damar shiga harkokin ƙungiyoyi da bayar da gudummawa wajen yanke shawara.
A cewarsa, ya kamata ƙungiyoyin ƙwadago su kasance wakilan muradun dukkan mambobinsu, maimakon su mayar da hankali kan muradun wasu tsirarun mutane.
Ya ƙara da cewa akwai buƙatar ƙungiyoyin su sake duba tsarin shugabanci da wakilci domin samun ingantacciyar hanyar magance matsalolin ma’aikata.
A ƙarshe, VCT Forum ta sake jaddada buƙatarta ta inganta albashin malamai, samar da kyakkyawan yanayin aiki da tabbatar da shugabanci mai adalci a ƙungiyoyin ƙwadago.
Ƙungiyar ta bayyana cewa zuba jari wajen inganta walwalar malamai yana da muhimmanci matuƙa wajen ƙarfafa harkokin ilimi da tabbatar da ci gaban Jihar Kano.

