eMagazine Media Channel LABARAI SHUGABAN NUT YA SAKE GABATAR DA KORAFIN MALAMAI GA GWAMNA ABBA, YA NEMI A BIYA SHUGABANNIN MAKARANTUN SAKANDARE KUDIN DUTY POST
LABARAI

SHUGABAN NUT YA SAKE GABATAR DA KORAFIN MALAMAI GA GWAMNA ABBA, YA NEMI A BIYA SHUGABANNIN MAKARANTUN SAKANDARE KUDIN DUTY POST

IMG 20260721 WA0057

SHUGABAN NUT YA SAKE GABATAR DA KORAFIN MALAMAI GA GWAMNA ABBA, YA NEMI A BIYA SHUGABANNIN MAKARANTUN SAKANDARE KUDIN DUTY POST

Daga Umar Tijjani Isah, Shugaban Yada Labarai na NUT

Shugaban Ƙungiyar Malamai ta Najeriya (NUT), reshen Jihar Kano, Comrade Baffa Ibrahim Garko, ya sake gabatar da buƙatu da korafe-korafen malaman makaranta ga Maigirma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, inda ya roƙi gwamnatin jihar da ta gaggauta magance wasu muhimman matsalolin jin daɗin malamai da suka daɗe suna jiran kulawa.

IMG 20260721 WA0056

A yayin ganawar, Shugaban NUT ya roƙi Gwamnan da ya ba da kulawa ta musamman ga waɗannan muhimman buƙatu:

A ke biyan kuɗaɗen School Upkeep na makarantun sakandaren gwamnati a faɗin Jihar Kano domin inganta gudanar da harkokin makarantu.

A fara biyan kuɗin Duty Post Allowance ga shugabannin makarantun sakandare (Principals), kamar yadda ake biyan takwarorinsu na makarantun firamare.

A daidaita albashin malaman firamare da na sakandare a Jihar Kano domin tabbatar da adalci da daidaito a cikin aikin koyarwa.

Da yake mayar da martani, Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa Shugaban NUT cewa gwamnatin jihar za ta yi nazari mai zurfi kan dukkan buƙatun da aka gabatar tare da ba su kulawar da ta dace.

Haka kuma, Gwamnan ya yaba wa shugabancin NUT bisa jajircewarsa wajen kare haƙƙoƙi da inganta walwalar malamai, tare da yi wa Shugaban ƙungiyar fatan alheri da nasara a kokarinsa na ci gaba da wakiltar muradun malaman jihar.

Wannan ganawa ta sake nuna ƙudirin Ƙungiyar NUT na ci gaba da fafutukar ganin an inganta yanayin aikin malamai da walwalarsu, tare da fatan cewa cika waɗannan buƙatu zai ƙara ƙarfafa tsarin ilimi da inganta gudanar da makarantu a Jihar Kano.

Shugaban ƙungiyar ya bayyana hakan ne a wajan taron ba wa sabbin Malaman makaranta da gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf ya dauka a dukkanin matakan ilimi na jahar Kano, wanda gudana a Rufaffen dakin taro na Sani Abacha stadium dake kofar Mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version