Education

KERD: Quality Assurance ta kai ziyarar duba aiki makarantar Hasiya Bayero GGASS, ta yaba wa Malamai bisa jajircewarsu wajen aiki

IMG 20261019 WA0003
IMG 20261019 WA0003

Quality Assurance t ta kai ziyarar duba aiki makarantar Hasiya Bayero GGASS, ta yaba wa Malamai Bisa jajircewarsu wajen aiki

Jami’an Kula da Ingancin Ilimi (Quality Assurance) ta Hukumar KERD ta kai ziyarar aiki makarantar Hasiya Bayero Girls’ Government Arabic Senior Secondary School (GGASS) a ranar Litinin 19/10/2026, a wani yunƙuri na sa ido kan ayyukan koyarwa da koyo, tare da tabbatar da bin ƙa’idojin ilimi a faɗin Jihar Kano.

A yayin ziyarar, tawagar ta lura cewa malamai suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, tare da nuna jajircewa wajen sauke nauyin da ke kansu da kuma samar da ingantaccen tsarin koyarwa da koyo.

Jami’an sun tantance ayyukan makarantar tare da bayar da shawarwarin ƙwararru da za su taimaka wajen ƙara inganta ilimi da samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa a makarantar.

Shugabar makarantar, Hajiya Rabi Abba Ahmed, ta yaba wa jami’an na Quality Assurance da kuma Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Gwani Dr. Ali Haruna Makoda, bisa kulawarsa ga ci gaban ilimi da ƙoƙarin da yake yi na inganta ɓangaren ilimi a jihar.

Haka kuma, ta miƙa saƙon godiya ta musamman ga Babbar Sakatariyar Hukumar KERD, Hajiya Rabi Inuwa Hussain, bisa ci gaba da goyon baya da ƙarfafa guiwar da take bai wa tawagar jami’an Quality Assurance wajen gudanar da ayyukansu.

A cewar shugabar makarantar, ayyukan sa ido da tantance ingancin makarantu da tawagar ke gudanarwa suna taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa shugabannin makarantu da inganta koyarwa da koyo a faɗin Jihar Kano.

Hajiya Rabi Abba Ahmed ta kuma bayyana godiyarta ta musamman ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa ƙoƙarin da yake yi na tabbatar da cewa ’ya’yan talakawa masu ƙaramin ƙarfi sun samu damar samun ingantaccen ilimi.

Musamman ma, ta yaba wa shirin gwamnatin jihar na ɗaukar nauyin kuɗin jarabawar kammala karatun sakandare (SSCE) ga ɗaliban Jihar Kano, tana mai bayyana cewa wannan mataki yana taimakawa wajen rage nauyin kuɗi da ke kan iyaye da masu kula da ɗalibai, tare da faɗaɗa damar samun ilimi.

Ziyarar ta jaddada muhimmancin ci gaba da sa ido kan ingancin ilimi, kulawa mai inganci ga makarantu, da haɗin guiwa tsakanin hukumomin ilimi da shugabannin makarantu wajen inganta matsayin ilimi a faɗin Jihar Kano.

E-Magazine Media Channel

Ilimi • Yaɗa Labarai • Wayar da Kan Al’umma

Domin neman karin bayani ko neman talla ko sanarwa , ku tuntuɓe mu ta wannan lambar wayar 08036614747

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *