Gwamnatin soja ta Burkina Faso ta tabbatar da tsare sojojin Najeriya 11 tare da kwace jirgin sojan saman Najeriya, bayan da aka zargi jirgin da shiga sararin samaniyar ƙasar ba tare da izini ba.

A wata sanarwa da ƙungiyar kasashen Sahel (AES) ta fitar da yammacin Litinin, ta ce jirgin C-130 mallakin rundunar sojin saman Najeriya an tilasta masa yin saukar gaggawa a garin Bobo Dioulasso a ranar 8 ga Disamba, 2025, saboda an ga jirgin yayin da yake shawagi a sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da izini ba.
Ƙungiyar AES ta ƙunshi Burkina Faso, Nijar da Mali – duk suna ƙarƙashin mulkin soja a halin yanzu.
Sai dai kuma rundunar sojin Nigeriya ta musanta zargin a inda su ka fitar da sanarwar a ranar Talata 9/12/2025. Daraktan Hulda da Jama’a na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce jirgin yana kan hanyar tafiya zuwa Portugal ne lokacin da aka gano matsala bayan tashi daga Legas.
NAF ta bayyana ce wa, jirgin ya karkata zuwa filin jirgin saman Bobo-Dioulasso a Burkina Faso bisa ƙa’idodin tsaro na zirga-zirgar jiragen sama na duniya ba wai kama shi aka yi ba.

NAF ta kara da ce wa, dukkan jami’an da ke cikin jirgin suna cikin koshin lafiya, kuma hukumomin Burkina Faso sun karɓe su cikin mutunci.
