Mun hada wa malam Haruna Bashir Muhammad kuɗaɗen da muka tattara masa bisa kissan gillar da aka yi wa iyalansa 7 ciki harda matarsa kuɗi sama da ₦25,215,258.45

A ranar Juma’a 23/1/2026 babban lauyan nan kuma ɗangwagwarmaya wanda aka fi sani da Barrister Abba Hikima Fagge ya mika wa Malam Haruna Bashir Muhammad wanda aka kashe masa matarsa da yayansa 6 a unguwar Chiranci Gabas gidan kwari dake karamar hukumar Kumbotso, jahar Kano.
Hikima ya ce tun lokacin da aka yi wa wannan bawan Allah ta’addancin kashe masa iyali ne muka nema da a taimaka masa . Wanda cikin ikon Allah aka taimaka masa. A inda wasu bayin Allah ma suka bashi kujerar zuwa maka. Hikima ya ce a wannan rana ta juma’a na tura wa wannan bawan Allah kuɗin da aka tattara masa ta cikin account dina kimanin sama da ₦25,215,258.45. Kuma ya ce sun je bankin shi Malam Haruna Bashir Muhammad a inda aka kulle masa account domin tabbatar da tsaron kuɗinnasa har zuwa lokacin da zai samu nutsuwa.
Baba Comrade, E-magazine
23/1/2026
